A Katsina: Shirin BASDA ya inganta ilimi a jihar

A Katsina: Shirin basda ya inganta ilimi a jihar

A Katsina: Shirin basda ya inganta ilimi a jihar

Tura wannan Sakon

Daga Muawuya Bala Idris,

Katsina Shirin samar da ilimi ga al’umma, Watau BASDA a turance yana aiki a jihohi 17 a Najeriya. Shirin wanda ake aiwalar da ayyukanta a qarqashin bakin duniya yana bayar de karfi wajen koyo da koyarwa, samar da ilimi ga kowa da kowa da kuma qarkafa yanayin ilimi don kawo ci gaba.

Jihar Katsina tana xaya daga cikin wacce ta ke cin moriyar Shirin.

An fara aiwatar da ayyukan shirin a shekara 2019, a inda aka zavo qananan hukomomi 22 domin magance matsalar rashin zuwa yara makaranta tare da zavo qananan hukumomin 13 domin koyar da karatu da rubutu ta hanyan shirin RANA.

Domin sanar da kyakyawan shiri, gwamnati jihar Katsina ta kafa kwamitoci guda biyu.

Kwamiti na farko yana qarqashin shugaban hukumar ilimin firamare, Lawal Buhari Daura, sannan kwamiti ne biyu yana qarqashin kwamishinan ilimi, Badamasi Lawal Charanchi.

A mataki na farko an zavi makarantu 1,004 domin koyo da koyarwa da malamai 5,161 domin aiwartar da shrin koyar da rubutu da karatu a qarqashin shirin na RANA. Shirin BASDA cikin shekeru 4 da aiwatar da shi.

Ya kawo ci gaba wajen samar da yawan yara waxanda aka sa a makaranta. A qididiga an samu yin a rejistar yara fiye da 361,525a makarantu.

Haka kuma sama da makarantu allo guda 255 sun samu gajiyar shirin ta hanyar samar musu da ruwan sha da banxaki kuma kayan koyarwa da sutura ta yan makaranta (Uniform).

Wannan gajiya gu makarantu allo ta taimaka wajen sannar da yara su koyi karatun boko tare da yin rubutu kamar sauran takwarorinsu a sauran makarantu.

Haka kuma ta hana yin bahaya a waje da kuma samar da ruwa ga makarantu, wanda ya samar da yanayin koyarwa mai tsari: Madrasatul Ilmin Kur’an, na daya daga cikin makarantu da suka ci gajiyar aikin shirin BASDA.

Shugaban Makarantar, Malam Muhammed Unguwar Liman, ya yabawa shirin domin samar da abubuwa morai rayuwa ga xaliban tare dasanar da kayan koyo da koyarwa.

Ya ce, an samar da duban tabarmi ga xaliban da riguna domin inganta rayuwansu. Wani xalibi Ibrahim Musa ya ce, ya amfana da shirin BASDA ta hanyar koyon harshen Turanci da rubutu.

Ya ce, a yanzu, yana iya amfani da ilimin da ya samu domin ci gaba da karatu a matakin babbar makarantar sakandare. Shi kuma, shugaban qungiyar malamai ta jihar Katsina watau (NUT) rashen jihar Katsina, Muhammed Mai’adua, ya ce, malamai da yawa sun samu horo da samar musu da kayan aiki a qarqashin shirin.

Ya ce, shirin ya taimaka wajen qara kuzarin malamai su tafiyar da aikinsu. Da yake magana a kan shirin, shugaban hukumar ilimi ta jihar Katsina, Lawal Buhari Daura ya ce, a qarqashin shirin, jihar ta karvi kuxi dala miliyan 1,550,616 ga makarantu. Haka kuma ya ce, an samar da tabarmi har dubu 25,522, da kayan makaranta (Uniform) ga makarantu Kur’ani har dubu 30. Har ila yau, ya ce, shirin ya sanar da kayan aiki kamar kwanfutar (computer) da kayayyakin sadarwa na zamani ga malamai. Buhari ya ce, shirin ya horar da malamai dubu 7,378 da samar da gina ajujuwa, da kujeru ga makarantu har sittin (60).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *