A Kudancin Amurka: Neymar Ya Zama Na Uku A Cin Kwallaye

Tura wannan Sakon

Daga Hassan Muhammad

Brazil ta doke Tunisia 5-1 a wasan sada zumunta da suka fafata a Parc des Princes a birnin Paris din Faransa ranar Talata.

Neymar ne ya ci wa Brazil kwallo na uku a bugun fenariti a minti na 29 da fara wasa, kuma na 75 kenan da ya ci wa tawagar jumulla.

Sauran da suka ci wa Brazil kwallayen a wasan na sada zumunta sun hada da Richarlison da Pedro da kuma Raphinha, wanda ya ci biyu a karawar.

Neymar ya zama na uku a Kudancin Amurka a yawan cin kwallaye a tarihi,, bayan Lionel Messi na Argentina da Pele, tsohon dan wasan Brazil.

Kawo yanzu Neymar ya zura 75 a raga a wasa 121 da ya yi wa tawagar Brazil. Pele zakakurin dan wasan Brazil shi ne na biyu, wanda ya ci 77 a karawa 92 da ya yi wa kasarsa.

 Kyaftin din Argentina Lionel Messi shi ne na farko a yawan cin kwallaye a Kudancin Amurka mai 100 a raga, bayan wasa 164.

Brazil ta yi wasan na sada zumunta don shirin buga gasar kofin duniya da Katar za ta karbi bakunci a cikin watan Nuwamba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *