A manyan gasar Turai: Haaland na kan gaba a cin kwallaye

haland

haland

Tura wannan Sakon

Bayan da aka fara yin nisa a wasannin kakar bana a nahiyar Turai, fitila ta fara haska ‘yan wasan da ke takarar lashe takalmin zinare a gasar lik a nahiyar Turai.

Akan zabi duk dan wasan da ya zura kwallo mafi yawa a karshen kaka, domin yi masa kyautar takalmin zinare, idan an kammala wasannin.

Cikin manyan gasar Turai biyar da ke kan gaba a taka leda a duniya wato Premier da La Liga da Bundesliga da Serie A da kuma Ligue 1 a kan lissafi maki biyu ga kwallon da aka zura a raga.

Sabon dan wasan da Manchester City ta dauka a bana, Erling Haaland shi ne kan gaba a cin kwallaye a Turai mai 11 kawo yanzu.

A karshen mako City ta doke Wolverhampton 3-0, inda dan kwallon ya hada 11 a karawa bakwai a Premier, yana da maki 22 kenan.

Tsohon dan kwallon Borussia Dortmund ya ci kwallo uku rigis sau biyu da fara kakar nan, kuma shi kadai ne a manyan gasar Turai biyar da ya haura 10.

Robert Lewandowski na fatan lashe kyuatar karo na uku, sai dai yana biye da Haaland na City.

Cikin kwallo 18 da Barcelona ta zura a kakar nan, Lewandowski ne ya ci takwas yana da maki 16 kenan.

Neymar na Paris St Germain yana da maki 16 iri daya da na Lewandowski, inda dan wasan Brazil ya zura takwas a raga a Ligue 1.

Sauran da suke takara har da Kylian Mbappe na PSG da Aleksandar Mitrovic na Fulham da kuma Marko Arnautovic na Bologna mai kwallo shida kawo yanzu.

Harry Kane shi ne na biyu a Premier League a cin kwallaye mai shida a raga da tazarar biyar tsakaninsa da Haaland.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *