A Maulidin Inyass: Matawalle ya yi furuci kan hada kan Musulmi

A Maulidin Inyass: Matawalle ya yi furuci kan hada kan Musulmi

A Maulidin Inyass: Matawalle ya yi furuci kan hada kan Musulmi

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau Gwamna Bello Mohammed ya buKaci Musulmin Kasar na da su haDa kansu, domin haDin kai wajibi ne a tsakanin Musulmin Nijeriya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karBar baKuncin Mauludin bana na Sheikh Ibrahim Nyass, ya ce, bikin da ake gudanarwa duk shekara, wata hanya ce da Musulmin duniya ke haDuwa domin yabon Allah da manzonsa Annabi Muhammad (SAW).

Ya Kara da cewa, Mauludin na bana ya jawo hankalin dubban daruruwan jama’a a jihar Zamfara inda kowa ya shagaltu da addu’a da godiya ga Allah (SWT), shi ne abin da jihar ke buKata a wannan lokaci na jarabawar da a ke ciki. Matawalle ya ce “Ba zan yi Kasa a gwiwa ba wajen ba yar da damar gudanar da Mauludin na baDi idan kwamitin shirya taron ya buKace ni,” in ji gwamna Matawalle, ya kuma yi kira ga dukkan mahalarta Mauludin da su sadaukar da karfinsu wajen yin addu’o’in neman zaman lafiya da haDin kan Kasarmu.

Taron ya shaida naDin sarautar Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi na II a matsayin babban ubangida kuma jagoran Darikar Tijjaniyya a Nijeriya, muKamin da kakansa, Sarki Muhammadu Sanusi I ya riKe har zuwa rasuwarsa a farkon shekarun 1980.

A jawabinsa na karramawa, Muhammadu Sanusi 11 ya tabbatar wa Kungiyar a Nijeriya cewa, zai yi duk abin da ya kamata a gare shi wajen ciyar da mabiyansa gaba. Bikin ya samu halartar dubban Daruruwan mabiya Darikar Tijjaniyya daga sassan duniya KarKashin jagorancin shugaban Darikar Tijjaniyya na duniya, Sheikh Muhammad Mahi Nyass

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *