A Neja: Sarkin Daji ya tallafa wa mata dubu 3 -Da jarin dubu 50-50

Alhaji Abdulmalik Sarkin Daji,
Daga Danjuma Labiru Bolari, Gombe
Kw a m i s h i n a n ma’aikatar kananan hukumomi na jihar Neja, Alhaji Abdulmalik Sarkin Daji, ya tallafa wa mata fiye da dubu 3000 da jari na Naira dubu 50 kowacce cikin shekara 2 a matsayin jari domin saukake musu kuncin rayuwa.
Amina Abdulhamid Mina, Jakadiyar Malikiya, kuma shugabar mata ta kungiyar Dangin Juna Afirka Initiatibe, ne ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da wakilinmu a Gombe a lokacin wani taron manema labarai da ta kira kan irin ci gaban da sarkin Daji ya kawo wa mata a jihar.
Amina Abdulhamid, ta ce, a duk fadin jihar Neja babu wani dan siyasa ko matashi da ya ke da irin halinsa domin a cikin shekaru 2 na zamansa kwamishinan kananan hukumomi ne ya bar tarihin da ba za’a manta da shi ba.
Ta ce, a matsayin ta na Jakadiyar Malikiya ta hannun ta kawai ta rarraba wa mata kudi fiye da Naira
miliyan 3, domin su ja jari a yankin Mashegu da Maruga da Wushishi.
A cewarta bayan wadannan yankunan, alherinsa ya karade kaf illahirin jihar Neja wanda haka ta sa ake masa lakabi da farin jakada.
Ta yi amfani da wannan damar ta kirayi jama’ar jihar Neja da su yi koyi da irin halin Abdulmalik Sarkin Daji Fari mai farar aniya.
Sannan ta kirayi matan da ake bai wa tallafin da cewa, su dinga ririta wa, domin abinda suka samu domin su dogara da kansu domin ana ba su ne domin su samu madogara a rayuwa. Daga karshe, ta roki gwamnan jihar Neja da ya ci gaba da budawa kwamishinan domin ya ci gaba da tallafa wa marasa galihu, domin ragewa gwamnati dawainiya