A Nijar: Gwamnati ta horar da tubabbun ‘yan Boko Haram

‘Yan-ta’adda sun fi mu makamai, mun fi su jarumtaka -Bazoum

Shugaban Kasar Nijar Bazoum

Tura wannan Sakon

Jamhuriyar Nijar ta sanar da kammala horar da tubabbun mayakan Boko Haram fiye da 40 da aka sauya tunaninsu da kuma koya masu sana’o’i a karkashin wani shirin gwamnatin kasar.

Wani jami’in hukuma ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, tubabbun mayakan su 42 da suka samu horo kuma yanzu haka sun bar cibiyar horar da su da ke Goudoumaria a yankin Diffa a ranar Litinin da ta gabata.

Rahotanni sun ce, kowane daya daga cikin mutanen 42 ya karbi kayayyakin sana’ar da ya koya da suka hada da na gyaran mota ko babur ko dinki ko aikin kafinta da walda ko kuma kasuwanci.

Bayanai sun ce an kuma horar da su a kan yadda za su rage tsattsauran ra’ayin addini tare da rantsuwa da Alkur’ani cewa, ba za su sake daukar makamai domin tayar da hankali ba.

Kungiyoyin da ke da alaka da Al-Kaeda da ISIS sun dade suna kai munanan hare-haren ta’addanci a Nijar inda sukan kashe dubban rayuka a yammacin kasar, yayin da mayakan da ke da alaka da Boko Haram da ISIS ke kai hare-hare a kudu maso gabashin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *