A Nijeriya: 20 ga Yuli za a yi babbar Sallah -Sultan

Sarkin Musulmi a Nijeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bayyana Lahadi a matsayin 1 ga watan Zul-Hijja na shekarar hijira ta 1442, wadda ta yi daidai da 11 ga Yulin 2021.
Hakan na nufin za a gudanar Idin Babbar Sallah ranar Talata, 10 ga Zul-Hijja wanda ya yi daidai da 20 ga watan Yulin 2021.
Bayanin na cikin wata sanarwa da Farfesa Sambo Wali Junaidu ya sanya wa hannu, wanda shi ne shugaban kwamatin shawarwari na Fadar Sarkin Musulmi.
Al’ummar Musulmi na yin bikin Idin Babbar Sallah – ko kuma sallar layya – duk ranar 10 ga watan 11 na kalandar Musulunci.
Bikin na bana zai kasance cikin matsin tattalin arziki musamman sakamakon annobar korona da kuma faduwar darajar kudi a kasashe masu tasowa kamar Nijeriya.