A Nijeriya: Daina amfani da takardar kudi, da saura –Daurawa

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

Wani fitaccen dankasuwa kuma shugaban kamfanin General Merchant da ke kantin Kwari a babban birnin Kano, Alhaji Muhammadu Sagir Daurawa ya ce, kokarin da gwamnatin Nijeriya take yi wajen hana amfani da takardar kudi da kuma shigo da sabon wani salon tsari na cinikayya ta hanyar amfani da computer (E-naira) na bukatar lokaci domin har yanzu ba duka ‘yan Nijeriya ke amfani da computer ba.

Daurawa ya yi furucin ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilin jaridar Albishir a babban birnin Kano makon da ya gabata.

Ya ce, yunkurin da gwamnatin tarayya take yi wajen amfani da e-naira sakamakon takardar kudi zai samu cikas da kuma kalubale domin kasa har yanzu ba ci gaba musamman ta wajen wutar lantarki da harkar sadarwa da makamantansu domin a wannan kasa tun daga 1960 lokacin da aka samu ‘yancin kai har izuwa yanzu babu wani lokaci da aka samar da wutar lantarki ta wata daya cir ba tare da wata matsala ba, domin duk wani ci gaba a duniya yana tare da samar da wutar lantarki da kuma hanyar sadarwa ta zamani.

Alhaji Sagir Daurawa ya kara da cewa, a yanzu haka akwai shirye-shirye da tsare tsare domin ganin nan gaba an samar da shugabancin daga cikin kungiyar ‘yan kasuwa ko wanda ya san harkar kasuwanci ciki da bai.

Daga karshe, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yi wa kasa addu’a domin samun shugaba nagari a zabe mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *