A Nijeriya: Tsadar gas, kalanzir ta tilasta komawa kan gawayi

Gawayi
Daga Mahmud Gambo Sani
Baya ga tashin farashin man fetur da iskar gas da kuma kalanzir, farashin abinci na ci gaba da hauhawa a Nijeriya. Tashin farashin gas da kalanzir ya sa ‘yan Nijeriya da dama sun koma amfani da gawayi domin yin girki.
Wani magidanci ya shaida wa Albishir cewa, tsadar gas ce ta sa shi ya hakura ya koma amfani da gawayi. “Tun muna sayen gas a kan naira dubu 1600, ya koma Naira 2500 har ya haura ya koma Naira 4500, yanzu kuma ya haura Naira 4800”, in ji shi.
Sai dai yawan bukatar da ake yi wa gawayin ta sa farashinsa ya tashi a kasuwa. Ismaila Abubakar, mai sayar da gawayi ne a kasuwar Taurani da ke Kano, ya ce “A yanzu muna sayar da kowane kwano na gawayi Naira 200, muna sayar da buhun gawayi Naira 3000 zuwa 2800.”
Sai dai masana muhalli sun yi gargadin cewa, muddin ba a dauki matakin shawo kan tashin farashin gas da kalanzir ba, jama’a za su ci gaba da sare bishiyoyi, abin da zai haifar da gurbatar muhalli da kuma yunwa.
Dokta Salihu Umar Anka, babban jami’i ne a daya daga cikin kungiyoyi masu rajin kare muhalli, ya ce, suna cikin fargaba.
“Fargabarmu ita ce, ana tufka da warwara kenan, bayan ana ware kudi ana yi wa manyan kasashe alkawura cewa, ga abin da ake ciki cewa, mun dauki alkawuran za mu rage wadannan matsaloli, to sai ga shi talaka da kuma masu kudin na komawa amfani da itace. Masanin ya ce, wannan babbar barazana ce ga tsirran da ake da su.
Tsirran da ake da su na gargajiya suna taimakawa wajen dara kason noma domin a samu inganttaccen abinci. Ba za ka iya dakile sare bishiyoyi ba, idan baka samar da makamashi mafi sauki da mutum zai yi amfani da shi ba.