A Potiskum: Rashin motocin kashe gobara, barazanar rasa rayuka

Tura wannan Sakon


Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Al’ummar garin Potiskum cikin Jihar Yobe na nuna damuwarsu dangane da rashin motar kashe gobara mai inganci a garin wanda hakan kan haifar da barazanar rasa rayuka da dukiyar al’umomin garin.

Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin wani dan kasuwa, Alhaji Muhammadu Kabir mazaunin garin na Potiskum a tattaunawar sa da wakilinmu a garin na Potiskum.

Alhaji Muhammad Kabir ya kara da cewar, duk da cewa, garin na Potiskum shi ne cibiyar kasuwanci a jihar ta Yobe amma abin ban takaici motocin kashe gobara guda 4 ne garin uku manya daya kuma karama amma duka ukun manyan babu mai aiki ko daya duka sun lalace illa karamar motar wace ita din ma ba ta wani aiki na azo a gani.

Malamin ya kara da cewar, a makon da ya wuce wani bangare na babbar kasuwar garin na Potiskum ya kama da wuta sai da gobarar ta shafe sama da awanni uku tana ci da wuta da kyar aka samu damar kashe ta wajen shaguna 80 ne suka ƙone wadda inda ace wadancan motocin kashe gobarar na aiki da wuya barnar ta tsananta.

“A cewar Malamin har wayau a wannan mako aka kira shi a waya cewar wasu yara uku sun fada rijiya a wajen unguwar da kabarin tsohon Gwamnan marigayi Mamman Ali ya ke kasancewar shi shagon sa na kusa da yankin da ofishin hukumar jami’an kashe gobarar ya ke don ya je ya sanar musu don kai dauki, amma ya na zuwa ofishin ya sanar da su halin da ake ciki sai nan take daya daga cikin jami’an da ya tarar ya kada baki ya ce a gaskiya ba su da motar da za su je har can sai dai a dauka musu babur din adadaidaita sahu don ya kai su, hakan aka yi, amma kafin nan sai da ya tambaye su akan ko me ya samu wadannan motoci da ke tsaye sai aka sanar da shi cewar a dukkan su sun lalace, ku mutanen gari ku ya kamata ku koka ga gwamnati ko azo a gyara su.”

Don haka a cewar malamin wannan lamari yana ba su takaici ace duk girman garin na Potiskum ace babu wata muhimmiyar motar kashe gobara ciki alhali a kullum sai ka ga manyan jami’an gwamnati na gasar sayen manya-manyan motocin alfarma suna hawa alhali ga muhimman ayyukan da ya dace su yi don tserar da rayuwa da dukiyoyin jama’ar da suke mulka. Don haka suna rokon gwamnatin Jihar Yobe da ta yi wa Allah ta kawo musu dauki a garin na Potiskum ta wajen kawo musu sababbanin motocin kashe gobara ko kuma a gyara musu tsoffin motocinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *