A ranar matasan ta duniya: Sanata ID Gyan ya ziyarci matasa

Sanata ID Gyan ya ziyarci matasa
Daga Mohammed Ahmed Baba Jos
Sanata ID Gyan mai wakiltar Filato ta Arewa ya shiga sahun al’ummar duniya domin ta ya matasan murnar ranar, sanatan yayi bikin ne tare da matasan, a wannan shekara ta 2021, kuma ya amince cewa, kungiyar(United Nation) ta kirkiro ranar ne domin wayar da kan matasa da jawo hankalin jama’a, domin bai wa matasan gudunmawa su zama masu rike hannun jari, da samun mafita ga kalubalen da suke fuskanta a duniya, bikin yana canja tsarin matasan, Sanata Gyan ya bayar da shawara a kan aikin gona da kasuwanci ga matasa.
Nijeriya ba ta ci gaba da kasancewa mai rauni a cikin kasashen Duniya ba, da samar da wadataccen abinci, sannan ya nuna takaicinsa a kan masu lalata amfanin gona, hakan yakan hana samun wadataccen abinci, Sanata Gyan ya gana da matasa.
A lokuta daban-daban kuma ana yaba masa sosai yadda yake kokarin tallafa masu da abinda ya shafi karatu ko sana’a kuma lokuta da dama yana ziyartar mazabarsa ta filato ta Arewa domin jin korafin jama’arsa, kuma‘yan mazabar ne da kansu suke bayar da shaidarsa musamman a Jos ta Arewa, su kan ce, duk abin da ya faru ya kan zo, ko ya turo wakili, kamar a bara an sami ambaliyar ruwa a unguwar Zinariya da ke Jos ta Arewa inda ya baiwa wadanda abin ya shafa gagarumar gudunmawa ta kudi, don gina inda suka yi asara.
Shi dai Sanata ID Gyan dan jam’iyyar PDP ne, kuma yana wakiltar Filato ta Arewa, kamar kananan hukumomin Jos ta Arewa, Jos ta Kudu, Jos ta Gabas, Bassa, Riyom, da Barikin Ladi, kuma ya fuskanci kalubale a wadansu yankuna.