A sabon garin Zariya: Makanikan Keke Napep sun yi taron cika shekara uku

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

Hadaddiyar kungiyar makanikai da suke suke gyara Keke Napep da babur da kuma injin jannareto shiyya ta uku a karamar hukumar Sabon gari, sun yi taron murnar cikarsu shekara uku da kafuwa da kuma karrama wasu fitattun al’umm da suke tallafa ma su ciki har da Sarkin Kwangila Alhaji Abdullahi Sale.

A jawabina bayan ya karbi karramawar da kungiyar ta yi ma sa, Sarkin Kwangila Alhaji Abdullahi Sale, da farko dogon jawabi yay i kan muhimmancin sana’a ga matasa, inda ya bayyana cewar, shi kansa tun ya na yaro ya koyi sana’ar walda, wanda a cewarsa har makarantar koyon sana’a ya halarta inda ya kara kwarewa kan sana’ar walda a shekara fiye da talatin da suka gabata.

Alhaji Abdullahi, ya kuma nuna matukar gamsuwarsa na yadda shugabannin wannan kungiya ke koyar da matasa wannan sana’a ta makanike, ya ce babu ko shakka, duk al’ummar ta sami ci gaba matasan da suke cikin ta sun rungumi sana’ar dogaro da kai ne.

A kan haka ne ya yi kira ga iyayen yara ban a garin Kwangila kawai ba, da su kara azzamar tashi tsaye, na ganin sun dora yaransu a kan sana’ar dogaro da kai, ko da kuwa, a cewarsa, yaransu na karatun addini ko kuma na zamani. Da kuma ya juya ga karramawar da aka yi ma sa, Sarkin Kwangila Alhaji Abdullahi Sale, ya ce wannan kaimi suka yi ma sa kara tashi tsayi, na ci gaba da gudanar da shugabanci abin koyi a wannan gari na Kwangila, ta yadda za a ci gaba da samun ci gaba fiye da yadda aka samu a halin yanzu.

Tun farko a jawabinsa, shugababan kungiyar a karamar hukumar Sabon gariAlhaji Injiniya Abdulsalam Mohammed ya sun shirya wannantaro, domin waiwaye adon tafiya kan ayyukan da suke aiwatarwa da suka shafi ci gaban kungiyar da ‘ya’yan kungiyar da kuma yadda za a kare abokan hulda da suke kawo ma su abubuwan hawansu, domin gyara.

Sauran ayyukan da wannan kungiya ke aiwatarwa a cewar shugaban, a kwai daukar nauyin yaran da ake koya ma su sanna’ar kanikanci na su ci gaba da karatun addini da kuma na zamani ako wane mataki na ilimi, musamman yaran da suka fahimci iyayensu ba su da karfin daukar nauyin karatunsu. Ga manya da suke gudanar da wannan sana’a kuwa,amma bas u da ilimin addini da na zamani, a nan ya ce, su kan ba su shawarar ci gaba da neman ilimin da zai yi ma su jagorarar wannan sana’a da suke yi, wannan, a cewar shugaban kungiyar sun sami nasarori a wannan bangare da ba zai misiltu ba.

A game da matakan da suke dauka domin tsame baragurbi a wannan sana’a da suka runguma kuwa, Injiniya Abdulsalam ya ce, a kwai matakai da yawa da suke dauka domin gyara halayen mambobinsu da suke da wannan hali mara kyau, kamar yadda ya ce, in matsalar ta fi karfinsu, ba tare da bata lokaci ba, su kan mika wanda suka lura zai bata ma su sana’a ga ‘yan sanda, domin su dauki matakan da suka dace.

Shi ma a jawabinsa, Sardaunan Kwangila Alhaji Bello Abdullahi Alkali, yaba wa shugabannin wannan kungiya yay i na yadda suke da dokoki da tsare – tsaren kare mutuncin sana’arsu da kare mutuncin abokan huldarsu da kuma fitar da hanyoyin da suke tallafa wa junansu, musamman ta bangaren ilimi.

Sardaunan Kwangila ya bayyana nasarorin da wannan kungiya ta bayyana ta samu, ta sami nasarorin ne a dalilin kyakkywar shugabancin Sarkin Kwangila Alhaji Abdullahi Sale, ta yadda ba shi da lokacin kansa dare da kuma rana, sai me zai aiwatar domin ci gaban wannan gari, musamman yadda ya ke jawo kungiyoyin da aka kafa su domin ci gaban al’umma ko kuma domin ci gaban wannan gari na Kwangila.

Sauran wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun hada da wakilin babban kwamandan ‘yan sanda mai kula da shiyyar Zariya Alhaji Surajo Fana da shugaban kungiyar Makanikai na karamar hukumar Zariya, Injiniya Isa Ibrahim da kuma ma su sayar da kayayyakin gyaran Keke Nepep da Babura da kuma na’urar iannareto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *