A Sakkwato: Hukumar alhazai za ta mayar wa mahajjata kudadensu

Musa Lemu Daga Sakkwato
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Sakkwato ta kammala dukkan shirye shiryenta domin biyan maniyyatan da ba su sami damar sauke farali ba a shekarar 2022.
Bayani ya fito daga wajen babbab sakataran hukumar da ke Sakkwato, Alhaji Shehu Muhammad Dange a yayin da yake zantawa da manema labarai a karshen makon da ya gabata a Sakkwato.
Ya ce, tuni hukumarsa tare da hadin gwiwar ta kasa suka kammala shirye-shiyen biyan kudaden ga maniyyata hadi da wadanda ba su sami damar zuwa Madina ba.
Alhaji Shehu Dange ya ce, gudanar da aikin hajjin bana 2022 ya kasance jigila ne na gaggawa bayan da ita hukumar Saudiya ta bayar da sanarwar dage takumkumi domin gudanar da aikin hajji.
Babban Sakataran ya ce, duk da cewa, gudanar da ayyukan ya kasance na gaggawa, hukumarsa ta sami nasarori ganin cewa, babu wani ko wadansu alhazai da suka koka ta fuskar matsaloli.
A nan ya yi kira ga al’ummar Sakkwato da su ci gaba da bayar da hadin kai ga hukumar domin samum ci gaba da ayyukanta mai dorewa.
Daga karshe, Dange ya bayyana cewa, mahajjata 2483 ne suka gudanar da ayyukan hajjin shekarar 2022 a inda ake sa ran cewa, aikin hajjin 2023 zai zarce na shekarar 2022