A Sakkwato: Hukumar kidaya ta ja damarar kidayar gwaji -Ta ware gidaje fiye da dubu 7

Hukumar kidaya
Musa Lemu Daga Sakkwato
Hukumar kidaya ta kasa ta ware gidaje 7,718 domin gwaji kafin fara kidaya a cikin watan Afirilu na shekarar 2023.
An zabi wuraren domin gwaji ta yadda za a kai ga sun nasara kafin fara babbar kidaya a shekara mai zuwa.
An zabi wurare daban daban a dukkan fadin tarayyar Nijeriya daya hada da babban birnin tarayya Abuja a inda gudanar da haka shi ne zai bayar da tabbacin samun nasara a babbar kidayar da za a gudanar wanda hakan zai samar da kyakkyawar mafita da zai kawar da dukkan wani kalubale.
A yayin da yake bayani ga manema labarai a Sakkwato a maimakon shugaban hukumar na kasa, Malam Nasir Isa Kwarra a ranar Litinin da ta gabata kan shiye-shiryen hukumar babban kwamishinan tarayya a hukumar kidayar da ke Sakkwato, Alhaji Chiso Abdullahi Dattijo ya ce, domin cim ma nasara hukumar ta koyar da malaman kidaya domin tabbatar da sanin makamar aiki.
Babban kwamishinan ya ce, tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da a gudanar da aikin kidayar gwaji, kafin fara babbar kidayar cikin watan Afirilu 2023, a inda hakan ya bai wa hukumar dama ta fara killace wurare domin gwajin.
Ya ce, an fara gwajin kidayar gidaje daga ranar 27 ga watan Yuni zuwa 30 ga watan Yuli 2022 wanda hakan za a kai ga sanya nambobi a gidaje da kidayar jama a.
Malam Nasir Kwarra ya ce, an cim ma dukkan nasarorin shirye-shiryen da hukumar ta gudanar a saboda haka ya yi kira da dukkan masu ruwa da tsaki musamman gwamnati da kananan hukumomi da sarakunan yankin da aka ware gidaje domin gwaji da su bayar da tabbataccen hadin kai tare da taimaka wa malaman kidaya da aka tura yankunansu.
Daga karshe, Malam Nasir Isa Kwarra ya kara yin kira ga jami’an tsaro da su kula tare da sanya idanu ga malaman kidayar domin gudanar da ayyukansu cikin nasara.