A Sakkwato: Ma’aikatan lafiya sun yi barazanar tsunduma yajin aiki muddin…

Gwammna Tambuwal

Tura wannan Sakon

Musa Lemu Daga Sakkwato

Kungiyar ma’aikatan lafiya ta jihar Sakkwato ta bayar da wa’adin kwanaki 7 kacal ga gwamnatin jihar da ta cika mata alkawarin da kungiyar ta nema ko ta tsunduma yajin aiki har sai illa masha Allah .

Shugaban kungiyar na jihar, Malam Abdullahi Aliyu Jungle ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala taron kungiyar a ranar Lahadin da ta gabata a Sakkwato.

Abdullahi Aliyu Jungle ya ce, daukar matakin ya zama wajibi ganin yadda gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu da dukkan bukatunsu. Ya ce, kungiyar ta bayar da kwanaki bakwai daga ranar da ta yi zaman tattaunawarta a ranar 16 ta bayar da wa’adin zuwa 23 ga watan Oktoba, 2022.

Ya ce, ma’aikatan lafiya sun kasance a baya ta fuskar albashi a inda ma’aikaci da ke matakin albashi na 12 yake karbar dubu N8000 kacal a inda takwaransa da ke aiki a karkashin gwamnati jiha da ke matakin albashi na 9 yake karbar dubu N80.

Shugaban kungiyar ya ce, an mayar da su saniyar ware babu albashi mai ma’ana babu ciyar da su gaba duk da cewa, a kan tantancesu a duk shekara amma babu biyan bukata.

A saboda haka ba gudu ba ja da baya har sai an biya masu dukkan bukatunsu domin kungiyar ta tabbatar cewa, a kwai kudade da aka ware domin biya masu bukatunsu .

Ya ce, kungiyar ta fa hinci cewa, gwamnati ta amince da a biya masu dukkan bukatunsu kazalika da ciyar da su gaba amma abin yaci tura.

Kungiyar ta kalubalanci hukumar da ke kula da ma’aikatar lafiya nayin zagon kasa ga wadansu shirye-shirye da gwamnatin jihar ta sanya gaba. Daga karshe, kungiyar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta mayar da ma’aikatan lafiyar zuwa kananan hukumomi 23 kamar yadda suka kasance a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *