A Sakkwato: Mata 350 sun ci gajiyar asibitin Maryam Abacha

A Sakkwato: Mata 350 sun ci gajiyar asibitin Maryam Abacha
-Masu fama da yoyon fitsari
Musa Lemu Daga Sakkwato
Asibitin mata da kananan yara na Maryam Abacha dake Sakkwato ya yi wa mata dake da matsalar yankan gishiri watau yoyon fitsari aiki su kimanin 350 cikin majinyata 420 da aka kwantar a dalilin wannan matsala daga shekarar 2020 zuwa 2021.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban asibitin, Dokta Bello Lawal a lokacin da yake amsa tambayoyin manema Labarai a Sakkwato ranar Talatar da ta gabata
Babban likitan ya ce, samun nasarorin ya biyo bayan nuna kulawar gwamnatin jihar ga asibitin .
Dokta Lawal ya bayyana cewa gwamnatin jihar Sakkwato tare da hadin gwiwar NFPA sun kara inganta asibitin wajan tafiyar da ayyukansa na yau da kullum daya kunshi sake fasalin dakunan kwantar da majinyata, kazalika da samar da sababbin kayayyakin aiki na zamani.
Babban likitan ya tabbatar cewa a yanzu asibitin ya kasance daya daga cikin asibitocin da za a iya alfahari da su.
Dokta Lawal ya tabbatar cewa likitocin asibitin na gudanar da ayyukansu na yau da kullum har na tsawon sa’o’i 24 ba tare da nuna gajiya wa ba.
Ya shawarci majinyata da su kasance masu hakuri da dangana tare da nuna bukatunsu ko kuma korafi ga hukumar asibitin tare kuma da bin dukkan dokokin hukumar asibitin.
Ya kara da cewa, hukumar nan dake kasar Turai watau Spotlight tana taimakawa ainun tare da hadin gwiwar ma aikatar kula da harkokin mata dake jihar ta fuskar gudanar da wasu gyare- gyare a asibitin.
Daga karshe babban likitan ya shawarci al’ummar dake mu’amula da asibitin da su kasance masu fahimta ga dukkan ayyukan da asibitin ya sanya a gaba na yau da kullum.