A Sakkwato: Reshen ASUU ta ce a ja kunnen minista Ngige -Saboda yada karya

Yajin aiki: ASUU ta bayar da wa’adin makonni 3

Tura wannan Sakon

Musa Lemu daga Sakkwato

Kungiyar malaman jami’a reshen Sakkwato ASUU ta yi kira da gwamnatin tarayya da ta gaggauta jawo hankalin ministan kwadago da samar da ayyuka, Dokta Chris Ngige kan kalaman karya da yake yayatawa a gidan telabijin na Arise game da jami’ar Usumanu Danfodiyo da ke Sakkwato domin ka da karamar magana ta za babba.

A yayin da kungiyar take bayani ga taron manema labarai a Sakkwato a karkashin jagorancin shugaban kungiyar, Malam M N Almustafa, kungiyar ta bayyana cewa, minista Ngige ya karbi goron gayyata daga gidan telebijin na Arise a ranar 14 ga watan Yuli 2022 a inda ya fitar da kalaman karya a game da jami’ar Usumanu Danfodiyo Sakkwato cewa, wai jami ar tana ci gaba da gudanar da ayyukanta na yau da kullum.

Mista Chris Ngige ya ce, wai daliban da ke koyon aikin Likitoci na ci gaba da karbar darasi wanda hakan ba gaskiya ne ba.

Kungiyar ta bayyana cewa, ta yi mamaki kwarai cewa, babban mutum kamarsa da zai yi magana irin na dattijai amma sai bayyana karya da karairayi ga al’ummar kasar nan su sama da miliyan 200.

Mista Ngige ya yada karya cewa, wai mataimakin shugaban jami’ar Danfodiyo ya tabbatar masa cewa, jami’ar tana ci gaba da gudanar da ayyukanta na yau da kullum cewa, har ma ta yaye dalibai da ke karatu a fannin koyon aikin likitoci wanda hakan ya sa ya shawarci ministan kudi da ta shirya biyan jami’ar kudin da ya dace.

Kungiyar ta fito karara ta ce, Dokta Chris Ngige yana shirya bayanan karya ga shugaban kasa, Muhamadu Buhari tare da kirkiro bayanai na soki burutsu ga al’ummar kasar nan wanda hakan yake samar da illoli ga fannin ilimi.

A saboda haka kungiyar ta ce, babu wata takarda a rubuce da shi mataimakin jami’ar Usmanu Danfodiyo ya rubuta ko ya aika da wani wakili da sunan cewa, kwalejin da ke koyar da aikin koyon likitoci da ke jami’ar ba ta cikin yajin aiki wanda hakan ba gaskiya ne ba.

Kungiyar ta tabbatarwa Ngige cewa, babu wani malamin jami’ar Danfodiyo da aka biya albashi a inda suka tabbatar cewa, har yanzu malaman da sauran takwarorin su na nan daram kan bakan su har sai an biya masu bukatunsu.

A sanin kowa ne cewa, kungiyar ASUU ta fara yajin aikin ne tun a ranar 14 ga watan Fabrairu 2022 ba tare da nuna alamun janyewa ba, har sai ita gwamnatin tarayya ta duba dukkan bukatunsu.

Kungiyar ta shaidawa Dokta Ngige cewa, jami’ar Usmanu Danfodiyo ba ta yaye wadansu dalibai ba tun a lokacin da ta fara yajin aiki a cikin watan Fabrairu 2022.

A nan sai ASUU ta kalubalanci Ngige da ya fito domin nuna shaidar da zai iya kare kansa dangane da ire-iren wadannan karairayi da ya shimfidawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari kazalika da al’ummar Nijeriya.

Daga karshe, kungiyar ta bayyana cewa, Dokta Ngige yana yunkurin rarraba kawunan kungiyar da ke da kyakkyawan hulda da sauran abokanin huldarta da ke jami’ar domin kawai ya cim ma burinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *