A Sakkwato: ‘Yan-sanda sun shirya tsaf domin tinkarar zaben gwamna

Tura wannan Sakon

Musa Lemu Daga Sakkwato

Rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta ce, ta shirya tsaf domin tunkarar zabubbukan da ke tafe da ya shafi ‘yan takarar gwamnoni dana majalisun dokoki da za a gudanar a gobe Asabar 11 ga Maris 2023.

A lokacin da yake jawabi ga taron manema labarai a ranar Litinin da ta gabata a Sakkwato Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Malam Muhammad Usaini Gumel ya ce, sun shirya da duk wanda ya ce mata kule za ta ce masa cas.

Malam Usaini Gumel ya gargadi ‘yan siyasa da su kasance masu bin doka da oda domin cim ma nasarar gudanar da zabe mai inganci ba tare da tsangwama ko tashin tashina ba. Kwamishinan ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa, rundunarsa ta sami kyakkyawan hadin kan sauran jami’an tsaro da ke jihar da suka hada da sojoji da DSS da sauransu domin tabbatar an gudanar da zabe mai inganci. Kwamishinan ya kuma lashi takobi cewa, duk wanda hukumarsa ta kama da makami a lokacin gudanar zabe zai dandana kudarsa tare da ubangidansa. dukkan matsalolin da ke cim ma jam’iyyun tuwo a kwarya.

Ya ce, jami’an tsaro ba za su rungumai hannuwa suna kallon wadansu ‘yan tsirarun na ci gaba da aikata barna tare da yin barazana ga al’umma domin dogoro da ubangida, a saboda haka dukkan wanda aka kama yana neman kawo tashin hankali hukuma za ta hukunta shi hukunci mai tsanani.

A yunkurinta na tabbatar da samar da zaman lafiya ya sa rundunar ta ce duk wanda ya ce mata kule za ta ce masa cas. A samamen da rundunar take a wadansu wurare dabandaban a garin Sakkwato ta sami nasarar kama makamai iri daban-daban daga hannun ‘yan bangar siyasa da suka hafa da bindigogi kirar gida da adduna da gora da sauran su.

Daga karshe, rundunar ta kuma gudanar da taron gaggawa da masu ruwa da tsaki daga jam’iyyu daban-daban domin kokarin shawo kan matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *