A Samarun Zariya: ‘Yan-kasuwar tumatur sun koka kan tursasawa

kasuwar tumatur

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

Yan-kasuwar da suke sayar da tumatur da sauran kayayyakin abinci a filin masallacin da ke Samarun Zariya, sun koka da cewa, karfi da yaji ana neman a hana su ci gaba da gudanar da kasuwancinsu, bayan da suka kwashe shekaru fiye da 30 suna sana’ar.

Mai magana da yawun ‘yan kasuwar har ila yau mataimakin sakataren kungiyar ‘yan awo, bakin masallaci Samarun Zariya, Malam Umar Mohammed Junaidu ya bayyanawa wakilinmu da ke Zariya matsalolin da suke fuskanta a tsakaninsu da karamar hukumar Sabon Gari da ‘yan kwamitin masallacin Samaru da kuma jami’an tsaro.

Malam Umar Junaidu ya ci gaba da cewa, a cikin kwanaki 14 jami’an tsaron sa-kai da ‘yan sanda sun dirar masu a wurin da suke gudanar da kasuwancinsu, har ma da yi wa ‘yan kasuwa rauni a dalilin dukan da suka yi masu kan bukatar da lallai su tattara kayansu su bar wajen da aka ambata.

Mataimakin sakataren kungiyar ya ci gaba da cewa, babban limamin Samaru da kansa ya bayyana babu batun ‘yan kasuwar su bar wajen, domin harabar masallacin su suka mallaka ba karamar hukumar Sabon Gari ba ko kuma jami’an tsaron da suka ce, sun hana su sakat a harabar masallacin da suke cin abinci.

Malam Umar ya kara da cewa, saboda yadda matsalar ta yi kamari, ya sa dole suka shigar da kukansu a kotu, bayan kotun ta saurare su, kotun ta dakatar da umurnin da aka ba su da kuma zuwa da jami’an tsaro ke yi domin a kore su a wajen da suke zama.

Umurnin kotu nan a cewarsa sai suka wayi gari jami’an tsaro sun rufe kofofin da suke shiga, wanda ya haifar da zanga -zangar lumana da suka yi domin nuna rashin jin dadinsu da yadda aka hana su sukuni a wurin da suke gudanar da kasuwancinsu.

Barista Aminu Yahaya shi ne ke wakiltar ‘yan kasuwan a babbar kotun jihar Kaduna da ke Unguwar Turawa (GRA), ya shaida wa wakilinmu cewa, lallai ‘yan kasuwar ba su ba shi damar ya janye karar ba, kamar yadda ya ce, nan ba da jimawa ba za su sake bayyana a kotu, domin nuna wa kotun umurnin da ta bayar, ba a yi amfani da shi ba.

Barista Aminu ya kara da cewa, a matsayinsa na lauyan ‘yan kasuwar, ba su sami wata takarda mai magaa da yawun gwamnan jihar Kaduna ko hukumar tsara birane ta jihar Kaduna (KASUPDA) da ke yin bayani cewa ‘yan kasuwa da suke gudanar da sana’o’insu, su bar wajen ba.

A lokacin da wakilinmu ya yi ido hudu da shugaban karamar hukumar Sabon Gari, Injiniya Mohammed Usman, domin jin ta bakinsa kan matsalar, ya shaida wa wakilinmu cewa, shi ba zai yi magana a madadin hukumar Kasupda ba, kuma ba zai yi magana a madadin rundunar ‘yan sanda ba, kamar yadda ya ce, ba shi da alaka da su.

Injiniya Mohammed Usman ya kammala da tabbatar wa ‘yan kasuwar cewa, ya na shirye ya samar masu da wurin da za su ci gaba da harkarsu baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *