A Serie A ta bana: Mourinho ya fara darawa a wasan farko

A Serie A ta bana: Mourinho ya fara darawa a wasan farko

Mourinho

Tura wannan Sakon

Kungiyar da Jose Mourinho ke jan ragama Roma, ta fara Serie A ta bana da kafar dama, bayan da ta je ta doke Salernitana da ci 1-0.

Tun kan hutu Bryan Cristante ya ci wa Roma kwallon da ya sa ta hada maki uku a karon farko da fara Serie A ta kakar nan. Roma ta barar da damar maki, inda sabon dan kwallon da ta dauka a bana, Paulo Dybala ya buga kwallo ya doki turke da wadda Tammy Abraham ya buga aka tare.

Tsohon dan kwallon Manchester United da Chelsea, Matic ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka daya a Roma a watan Mayu. Shi kuwa Wijnaldum ya koma buga wasannin aro a Serie A daga Paris St Germain a makon jiya.

Shima Nicolo Zaniolo ya kusan ci wa Roma kwallo a karo da dama a wasa da Salernitana, wadda ta kai bantenta da maki daya kwal a bara, kaka ta uku kenan tana Serie A. Haka ma Nemanja Matic da Georginio Wijnaldum sabbi da suka koma kungiyar a kakar nan, sun buga wa Roma fafatawar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *