A Sham: Jaura ta halaka jariran ‘yan-gudun hijira

A Sham: Jaura ta halaka jariran ‘yan-gudun hijira
Jarirai biyu sun rasa rayukansu a sakamakon tsananin sanyi bayan saukar dusar kankara a kan tantunan ‘yan gudun hijira a arewacin Syria.
Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya (UN) ya fada wa kamfanin labarai na AFP cewa, jaririya mai kwana bakwai da kuma ‘yar wata biyu sun mutu a yankin Idlib.
Mutane akalla miliyan biyu da dubu 800 ne suke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira a yankin da ‘yan tawaye ke da karfi, bayan sun bar gidajensu sakamakon yakin basarar kasar na shekaru 10.
Da yawa na zaune ne cikin tsofaffin tantuna ba tare da kayan sanyi ba ko kuma makamashin dumama jiki.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, lamarin na kara kazancewa saboda tabarbarewar tattalin arziki a Syria, inda farashin kayan abinci ya ninka cikin shekara daya, da kuma karancin kudin bayar da tallafi domin sayen kayan sanyi da sauran bukatu.