A shekara ta 2020: ‘Yan-jarida 62 aka kashe a duniya

A shekara ta 2020: 'Yan-jarida 62 aka kashe a duniya

A shekara ta 2020: 'Yan-jarida 62 aka kashe a duniya

Tura wannan Sakon

Daga Yusuf Abdul-Salam

Hukumar Ilimi da Adabi (UNESCO) da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya(UN) ta bayyana cewa,a shekara ta 2020 an kashe ‘yan-jarida 62 sun kan bakin aikinsu a sassan duniya daban-daban.

Ta ce,daga shekara ta 2006 zuwa 2020 an kashe fiye da ‘yan-jarida 1,200 ba tare da an kama ko an hukunta wani ba. Kididdiga ta nuna cewa, a ranar ‘yan-jarida ta duniya,mai taken; kawo karshen cin zarafi da zaluntar ‘yan-jarida a fadin duniya,an bayyana bukatar da ke akwai ta a hukunta wadanda ke da hannu wajen ci zarafin ‘yan-jarida domin a tabbatar da adalci.

A sakonsa na ‘yan-jarida ta duniya,babban sakatasen majalisar duniya, Mista Antonio Gutteres, ya furta cewa,mafi yawan ‘yan- jaridar da aka kathe, an kashe su ne a bakin aikin dauko rahoto kan tashe- tashen hankulan jama’a,r yayin da adadin wadanda aka kashe ba a bakin aikinsu ba,ya karu sosai da sosai.

A mafi yawan kasashen duniya, gudanar da bincike kan cin-hanci da rashawa da take hakkokin dan-adam da gurbata yanayi kan sanya ‘yan- jarida gamuwa da tasku ta hanya sanya rayuwarsu cikin kasada, in li Babban Sakataren.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *