A shekarar 2021: Mun ceci dukiya fiye da Naira biliyan 1 -In ji SFS Saminu

A shekarar 2021: Mun ceci dukiya fiye da Naira biliyan 1 -In ji SFS Saminu

hukumar kashe gobara ta jihar Kano karkashin

Tura wannan Sakon

Daga Muhammad Mustapha Abdullahi

A ci gaba da ayyukanta na ceton rayuka da dokiyoyin al’umma hukumar kashe gobara ta jihar Kano karkashin jagorancin shugaba, Alhaji Hassan Ahmad Muhammad a shekara da ta gabata ta samu kiraye – kiraye daga cibiyoyin ta guda 27 da ke fadin jihar, wanda suka hada da kiran kashe gobara da na ceto a kan tituna da ramuka ko koramai.

A tattaunawar da muka yi da jami’an da ke kula da yada labarai a hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ya shaida mana cewa, sun samu kiraye – kiraye daga cibiyoyin su na ceto da kashe gobara da ke fadin jihar Kano guda 27.

Saminu Yusuf ya ce, a shekara 2021 da ta gabata mun karbi kira na kashe gobara guda 831, sai kira na neman agaji guda 818, sai kira wanda muke kiran karya ko na tsokana shi kuma mun samu kira sau 201, sai kira na fadawa ramuka da kududdufai wanda shi ma mun samu kira guda 113, wanda duk a cikin wadannan kira da ake mana na fadawa kududdufai da ramukan akwai akalla mutum 98 da suka rasa rayukan su, sai kira da aka yi mana na fadawa rijiya ko gini ya rufto wa mutane, wanda shi ma an kira mu sau 37, wanda a cikin 37, din da aka kira mu akalla mutane 27 sun rasa rayukan su sanadiyar fadawa a rijiya ko gini ya fado masu.

Saminu Yusuf ya kara da cewa, duka a shekarar da ta gabata, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta karbi kira na hatsarin hanya guda 655, sai kira na rushewar gidaje guda biyu wanda shi kuma ya faru ne a lokacin damuna, sai kuma mutane da muka dauka a kan hanya da suke faduwa sanadiyar rashin lafiya iri – iri akalla mutum 14, sannan mun yi ceto na mutane da wutar lantarki ta kama da mutane da ake kiran mu muje gidajensu mu dauko su a mace har mutum 6.

SFS Saminu ya ce, ba wai iya mutane taimakon mu ya tsaya ba, domin a shekarar da ta gabata mun samu nasarar ceton dabbobi, ta bangaren ci gaban raguwar hatsari da gobara a gaskiya an samu ba kamar shekara biyu da ta gabata ba, wannan shekarar an samu sauki da ci gaba sanadiyar wayar da ke da shawarwari da hukumar. Saminu Yusuf ya ce hukumar kashe gobara karkashin jagorancin Alhaji Hassan Ahmad Muhammad na amfani da wannan da ma wajen kira ga Al,umma da su rinka kula da yadda suke amfani da wuta, da kuma rage gudu da ababen hawa tare da kula da dokokin hanya, sannan Al,umma su rinka kula da yanda yaran su da suke zuwa wasa wajen koramu da kududdufai da sauran wurare masu hatsari A karshe hukumar kashe gobara ta jihar kano na amfani da wannan da ma wajen taya mai girma Gwamnan kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje murnar shi ga sabuwar shekara tare da Sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero da daukacin Al,ummar jihar kano baki daya murnar shiga sabuwar shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *