A shiyyar Hadejia: APC ta fara yakin neman zaben gwamna

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan, Dutse

A ranar Asabar 12 ga Nuwamba, 2022, jam’iyyar APC a jihar Jigawa ta kaddamar da yakin neman zaben gwamnan jihar, bisa jagorancin gwamna Muhammadu Badaru Abubakar, a garin Hadejia, kamar yadda jadawalin yakin neman zaben gwamnan jihar yake.

Tun da safiyar wannan rana, al’umma magoya bayan jam’iyyar APC suka fara tururuwa zuwa garin na Hadejia domin halartar taron, tare da shaida yadda taron zai kasance, musamman ganin cewa zaben shekara ta 2023 na kara matsowa.

Haka kuma, an gudanar da taron cikin nasara tare da bayyana irin ayyukan alheri da gwamnatin jihar ta gudanar bisa tutar jam’iyyar APC da kuma yin kira ga al’ummar jihar da su zabi jam’iyyar domin ta ci gaba da ayyukan raya kasa a fadin jihar.

A jawabinsa, gwamna Badaru Abubakar ya shaida wa magoya bayan jam’iyyar APC cewa, daga shekara ta 2015 zuwa wannan lokaci, gwamnatinsa ta yi abubuwa masu matukar amfani ga al’ummar jihar wadanda ba za a manta da su ba, saboda muhimmancinsu.

Gwamnan ya jaddada cewa, idan al’ummar jihar Jigawa suka sake zabar jam’iyyar APC daga sama har kasa, ko shakka babu za su ci gaba da shan romon dimukuradiyya musamman ganin cewa, dan takarar gwamnan jihar, Malam Umar Namadi Dan Modi mutum ne mai kishin jihar Jigawa, duba da yadda ya yi aiki da shi na tsawon lokaci.

An gudanar da jawabai muhimmai a wajen taron, magoya bayan jam’iyyar APC sun jaddada godiyarsu ga gwamnatin Badaru Abubakar, saboda ayyukan alheri da aka yi musu a shiyyar ta Hadejia tare da yin alwashin ganin sun sake zabar jam’iyyar APC domin ci gaba da amfana da ribar dimukuradiyya.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani kan sahihancin dan takarar gwamnan jihar ta Jigawa, Umar Namadi Dan Modi, shugaban kungiyar manoman jihar, AFAN, Alhaji Idris Yau Mai Unguwa ya ce, ko shakka babu, idan aka zabi Malam Umar Namadi, a matsayin gwamnan jihar Jigawa, za a ci gaba da rabauta da romon dimukuradiyya, musamman ganin cewa, mutum ne nagari kuma amintacce.

Ya ce, a na su bangaren na manoma, za su ci gaba da kokari wajen ganin jam’iyyar APC ta lashe zaben 2023 a jihar Jigawa domin za su kara amfana daga manufofin Malam Umar Namadi kan harkar noma, domin wadata jihar da kuma kasa da abinci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *