A soke lefe da kayan daki, a gyara sadaki -Sakamakon taro

Daga Hassan Falaki Kulkul
A makon jiya ne, jaridar Albishir ta yi tattaki, inda ta ziyarci taron wata-wata na wata kungiya ta masu dalilin aure, da take gudanar da taronta a makarantar Alhaji Sani Buhari Daura (Walin Daura) da ke unguwar ‘Yar Maishinkafi, karamar hukumar Gwale, cikin birnin Kano.
Taron ya sami halartar shugabannin riko na kungiyar, da sauran ‘ya’yan kungiyar na kananan hukumomin jihar Kano. A wajen taron, an gabatar da addu’o’i na musamman, ga tsohon shugaban kungiyar, Alhaji Danbala Warure,inda jaridar ta tattauna da wasu shugabannin mata, da suka hadar da; Hajiya Asabe Dandago, Hajiya Halima Rogo, da Hajiya Asma’u DawakinTofa, da Hajiya Rabi’atu Lawan Rijiya Hudu, kan zamantakewar aure, da yadda za a shawo kan maganin sake-saken aure, musamman a kasar Hausa.
Hajiya Dandago ta bayyana cewa, lamarin sake-saken aure abubuwa da dama ne suke kawo shi, a yanzu wannan abu ya tabarbare, domin a yanzu zawarawa sun ninka sosai, saboda mun tsinci kanmu a hali na tabarbarewar arziki, wanda wannan abu ya shafi duniya, sannan ga rashin juriya.
Ita kuma a nata jawabin, Hajiya Asma’u Dawakin Tofa, ta bayyana cewa, yawan mace-macen aure ya ninka, a sanadiyar tabarbarewar tattalin arzikin kasa, sannan mu a karkara rashin ilimin zamantakewa, da sanin rashin hakkin ma’aurata, miji bai san hakkin matarsa ba, ita ma ba ta san hakkin mijinta ba, musamman ga bangaren maza, hakki ya rataya a kansu na ciyarwa.
Haka nan, Hajiya Halima Rogo ta ce, maganin mace-macen aure shi ne, yin adalci tsakanin ma’aurata, da taimakekeniya a tsakanin ma’aurata.
A karshe, Hajiya Rabi’atu Lawan Rijiya Hudu, karamar hukumar Dala, ta shawarci iyaye da masu neman aure kan cewa, a soke lefe, kuma a sok kayan daki, nauyin ya koma kan mijin da zai auri matar, sannan a gyara sadaki yadda ya kamata.