A tabkin Chadi: Zulum ya gwangwaje masunta da Motoci 5

Tura wannan Sakon

Sani Gazas Chinade, Daga Maiduguri

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da tallafin motoci 5 da kudade ga wadansu masunta da ‘yan-kasuwa da ke yankin Tabkin Chadi.

Da yake gabatar da jawabi, gwamnan ya ce, tallafin da ake bai wa masunta da ‘yan kasuwar kifi, an yi haka ne domin a karfafa masu gwiwa wajen aiwatar da sana’arsu ta kamun kifi da rarraba kayayyakin kifin zuwa kasuwannin Arewa maso Gabas da ma wadansu sassan kasar nan cikin sauki.

Da yake bayar da tallafin ga masuntan, a garin Monguno, ya ce, harkokin tattalin arziki sun wargaje a jihar saboda hare-haren Boko Haram a kan ofisoshin sojoji da al’ummomin da ke gabar tabkin Chadi.” A cewarsa, hakan ya haifar da gudun hijirar mutane fiye miliyan 2 daga gidajensu.

Domin haka ya ja kunnen ‘yan kasuwar da suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi ta bin hanyoyin da suka dace ba tare da almubazzaranci ba. Da yake kokawa kan yadda ake kai hare-haren, ya ce, ka fin ta’addanci, ana sayar da busasshen kifi a wadansu sassan kasar nan da kuma wadansu kasashen makwabta da suka hada da Jamhuriyar Nijar da Chadi da Kamaru cikin sauki.”

Gwamna ya gargadi masu sana’ar kifi da su gudanar da duk wata huldar kasuwanci da za ta taimaka wajen tallafa wa kawar da ayyukan ta’addancin Boko Haram da ISWAP. Kada a yi wata haramtacciyar mu’amala da za ta kawo cikas ga tsaron lafiyar jama’armu,” in ji shi, ya kara da cewa, duk wanda aka kama yana hulda da masu aikata laifuffuka to zai yi wa kansa da kansa abin da zai kai shi shiga halin tsaka mai wuya”.

Saboda haka, ya bukaci ‘yan kasuwar da su bai wa sojoji da sauran jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da bayanai kan ayyukan ‘yan ta’adda da ake zargi. Gwamnan ya je Monguno ne domin sa ido kan yadda za a rarraba Naira miliyan 275 ga ‘yan gudun hijira dubu 90 da kuma sauran kungiyoyi masu rauni.

Tun a shekarar 2019, gwamnatin jihar ta tallafa wa ‘yan kasuwa da aka lalata masu sana’o’in dogaro da kai a tsawon shekaru 13 da rikicin da ya barke a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *