A Yemen: Za a mika ragamar mulki ga jagorancin hadaka

Shugaban Yemen Abedrabbo Mansour Hadi

Shugaban Yemen Abedrabbo Mansour Hadi

Tura wannan Sakon

Shugaban Yemen Abedrabbo Mansour Hadi ya sanar da shirin mika ragamar mulki ga sabon shugabancin hadaka domin jagorantar kasar a wani yanayi da yaki tsakanin dakarun kawancen kasashen Larabawa da ‘yan-tawayen Huthi ya ki ci yaki cinyewa.

A wani jawabi da shugaban ya gabatar ta gidan telebijin daga birnin Riyadh na kasar Makka jim kadan bayan kammala tattaunawa a zaman karshe na kokarin shawo kan rikicin Yemen, shugaban ya ce, abin da ya zame masa wajibi a yanzu shi ne mika karfin ikonsa ga sabon jagorancin kasar.

Tuni dai kasar Makka ta yi maraba da matakin shugaban tare da sanar da shirin tallafa wa kasar da agajin dala biliyan 3 kodayake hadaddiyar daular Larabawa ce za ta bayar da wani kaso na kudin.

Gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan kasashen duniya ta gamu da matsala ne sakamakon yaki da ‘yan tawayen Huthi masu samun goyon bayan Iran suka kaddamar wadanda ke rike da birnin Sanaa da kuma galibin yankunan Arewacin kasar duk da shigar kasar Makka wadda ta jagorancin kawancen dakarun kasashen Larabawa a shekarar 2015.

Tun a shekara ta 2015 shugaba Hadi ya bar Yemen tare da samun mafaka a kasar Makka lokacin da ‘yan tawayen suka kwace iko da birnin Aden mai tashar jiragen ruwa a kudancin kasar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *