A Yobe 2023: Masu ruwa-da-tsaki sun saya wa Buni fom

Masu ruwa-da-tsaki sun saya wa Buni fom
Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Yobe sun sa wa gwamna Mai Mala Buni (Chiroman Gujba) fom domin ya sake tsayawa takarar gwamna a zaben shekara ta 2023.
Wadannan masu ruwa da tsakin sun hada da shugabannin jam’iyyar a kananan hukumomi 17 da ke jihar da wakilan ‘yan kasuwa da shugabannin al’umma da kuma magoya bayan jam’iyyar APC daga tushe.
An gudanar da taron ne a dakin taro na Wawa da ke gidan gwamnatin jihar a garin Damaturu. Mataimakin gwamna, Honarabul Idi Barde Gubana (Wazirin Fune) ya mika fom din tsayawa takara a madadin masu ruwa da tsaki ga shugaban jam’iyyar APC na jihar, Honarabul Mohammed Gadaka domin gabatar A Yobe 2023: Masu ruwa-da-tsaki sun saya wa Buni fom wa gwamnan.
Gubana ya ce, irin ayyukan da gwamnan jihar ya yi a cikin shekaru uku da suka gabata ya kara musu kwarin gwiwa wajen siyan fom din takarar gwamnan jihar a karo na biyu.
Sun kuma yi kira ga magoya bayan jam’iyyar APC da kungiyoyi da sauran jama’a da su goyi bayan wannan yunkuri nasu dangane da rufa baya ga takarar gwamnan a karo na biyu a shekara ta 2023.
Mataimakin gwamnan ya kara da cewa “Manufar ita ce a kiyaye matsayin APC a matsayin iyali daya, mun tsaya tare.