A Yobe: DSS Ta Yi Taron Shekara-Shekara A Damaturu

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, a ranar Alhamis, ta fara taron daraktocin tsaro na jihohi karo na 9 a shiyyar Arewa maso Gabas, zango na uku, na shekara ta 2022, a Damaturu.
Taron wani bangare ne na kokarinta na duba dabarun inganta zaman lafiya da tsaro a yankin da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
A lokacin da yake bayani a wajen bude taron, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, wanda mataimakinsa Idi Barde Gubana ya wakilta, ya bayyana godiyarsa ga daukacin hukumomin tsaro na ganin an dawo da zaman lafiya a jihar Yobe.
Ya tuna lokacin da babban birnin jihar Yobe ya zama ba kowa saboda tayar da zaune tsaye da ‘yan tayar da kayar bayan suka yi.
A cewarsa, “idan muka tuna, dukkanmu muna sane da halin da muka shiga, Damaturu a wancan lokacin, galibi ba kowa, muka zama ‘yan gudun hijira, cikin ikon Allah da kokarin Mai girma shugaban kasa kuma babban kwamandan sojojin tarayyar Nijeriya, Muhammadu Buhari aka samu zaman lafiya, Alhamdulillahi”.
Buni ya yi maraba da mahalarta taron, inda ya bayyana shi a matsayin lokacin da ya dace, yana mai nuni da cewa, taron zai taimaka matuka wajen inganta harkar tsaro a kasar nan daga duk wani nau’i na miyagun laifuka.
Da yake jawabi tun da farko, daraktan hukumar tsaro ta farin kaya DSS reshen jihar Yobe, Yunusa Abdulkadir ya ce, taron na da nufin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro, yana mai nuni da cewa, ayyukan masu ruwa-da-tsaki kamar su; sarakunan gargajiya da malaman addini, da jami’an tsaro da ‘yan uwa mata da hukumomi da kungiyar ‘yan banga da kuma kafafen yada labarai yana da matukar muhimmanci ga hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Daraktan ya lura cewa, wasu daga cikin ‘yan kasar da suka gamu da ajalinsu a lokacin da ake tayar da kayar baya, kafin nan sun bukaci goyon bayan zamantakewar al’umma domin guje wa tabarbarewar doka da oda da ke haifar da wani kalubalen tsaro.
Ya yaba wa gwamnatin jihar Yobe da jami’anta bisa goyon baya da hadin kai, wanda a cewarsa ya ba su damar gudanar da ayyukansu.
A nasa bangaren, shugaban taron, wanda kuma shi ne daraktan hukumar tsaro ta DSS reshen jihar Bauchi, Hassan Abdullahi, ya bayyana cewa, makasudin taron shi ne, neman hadin kai da yin musayar gogewa a shiyyar da samar da mafita.
Ya bayyana garkuwa da mutane da fashi da makami da satar shanu da tayar da kayar baya da kuma ‘yan bangar siyasa a matsayin wasu daga cikin kalubalen tsaro da ake fuskanta a halin yanzu. Abdullahi ya yaba wa gwamnatin jihar Yobe bisa kyakkyawar tarba da aka yi masu a lokacin da suka ziyarci jihar.
Shugaban ya kuma yi amfani da damar wajen mika godiyarsa ga hukumar raya Arewa maso gabas (NEDC) bisa tallafin da take bai wa jami’an tsaro a yankin.
A madadin daukacin majalisun sarakunan gargajiya na jihar, Mai Martaba Sarkin Fika kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar, Dokta Muhammad Ibn Abali Muhammad Idrissa, ya yaba rawar ganin da jami’an tsaron na DSS ke takawa, inda ya ce, “A madadin sarakuna iyayen kasa, muna so mu yaba da gagarumin kokari da nasarorin da kuka samu wajen samar da zaman lafiya a jiha, a cikin shekaru 13 da suka gabata, wadda a baya wuraren na karkashin kungiyar Boko Haram, amma yanzu an samu kwanciyar hankali matuka.”
Sarkin ya bayar da tabbacin cewa, “Muna tabbatar muku cewa za mu tallafa muku dari bisa dari, mu ba ku hadin kai domin samun nasara, muna muku fatan tattaunawa mai amfani”.
Sauran shugabannin hukumomin tsaro da suka fadi albarkacin bakinsu sun hada da ’yan sanda da Sojoji da hukumomin NSCDC da FRSC da NIS da NDLEA da NAPTIPP da NEDC da kuma sauran masu ruwa-da-tsaki.
Shugaban taron ya gabatar da wata takardar karramawa ga Mai Martaba Sarkin Fika kuma shugaban majalisar sarakunan jihar da kuma wakilin sarkin Damaturu.