A Yobe: Gwamna ya gwangwaje zawarawa 400, marayu 200 da tallafi

Tura wannan Sakon

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya umurci ma’aikatar samar da arziki da ayyukan yi da ta baiwa zawarawa 400 kayan tallafi don dogaro da kai.

Buni ya bada umarnin ne a lokacin da ya karbi bakuncin marayu 200 daga kananan hukumomi 17 na jihar. Gwamnan wanda ya tallafa wa marayu 200 da kudi Naira 50,000 kowannensu, ya ce sun cancanci kulawa daga gwamnati da sauran al’umma, inda ya ce ya zama wajibi a tallafa tare da baiwa marayu da sauran marasa galihu don samu dogaro da kan su.

“Shawarar da muka yanke na tallafa wa marayu, zawarawa a cikin sauran kungiyoyi masu rauni shine mu ba su jarin farawa don dogaro da kai musamman lura da halin rayuwa da ake ciki da ya shafi duniya baki daya.”

“Dole ne mu hada karfi da karfe don taimakawa wadanda suka rasa iyayensu a tsawon shekaru goma da aka kwashe ana fama da ta’addanci a fadin jihar.”

Ya kuma yabawa gidauniyar Kasar Katar bisa tallafin da ta bayar na kayayyakin more rayuwa ga marayu da marasa galihu a fadin jihar.

Kodinetan shirin kuma mai bawa gwamna shawara na musamman kan harkokin addini, Ustaz Babagana Mallam Kyari ya yabawa gwamna Buni bisa yadda yake nuna sanin ya kamata ga marayu da zawarawa a jihar.

“Wannan shi ne karo na biyu da mai girma gwamna ke tallafa wa wasu marayu 200 kai tsaye da kudi. in ji Babagana Kyari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *