A Yobe: Gwamnati Ta Gina Cibiyoyin Kiwon Lafiya 178

Tura wannan Sakon

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

A kokarin da ta ke yi don samar da yanayin kiwon lafiya mai inganci ga al’umma Gwamnatin Jihar Yobe ta gina kanana cibiyoyin kiwon lafiya guda daya ga dukannin mazabun Jihar 178.

Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin kwamishinan ma’aikatar kiwon lafiya a Jihar Dakta Muhammad Lawan Gana a tattaunawar sa da manema labarai a babban dakin taro na Mai Mala Buni da ke sakatariyar kungiyar ‘yan jaridu NUJ da ke garin Damaturu.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa, bayan haka kuma har ila yau gwamnatin karkashin Mai Mala Buni ta kuma kara daga daraja wasu manyan asibitocin Jihar guda hudu na garuruwan Potiskum, Gashuwa, Geidam da Buni Yadi ya zuwa asibitoci na musamman (YSSH) don ragewa al’umma wahalhalun da suke samu ya zuwa wasu asibitocin garuruwa Jihohin makwabta irin su FMC Azare a Jihar Bauchi da kuma FMC Gombe don yin jinya.

Haka nan gwamnatin ta kuma daga darajar wasu manyan cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko (PHC) da ke garuruwan Machina, PHC Asibitin Malam Baba Nguru, PHC Yunusari, PHC Jajimaji, PHC Babangida, PHC Bara, PHC Buni Gari, PHC Yusufari matsayin manyan asibitoci, General Hospitals don saukaka wa al’umma.

Don haka ta bangaren kiwon lafiya gwamnatin Yobe ta yi matukar taka rawar gani musamman lura da kokarin da Gwamna Mai Mala wajen cika alkawuran da ya dauka a yayin yakin neman zaben sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *