A Yobe: Hauhawar zazzabin cizon sauro ta ragu -In ji Kundi Machina

Tura wannan Sakon

Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

A jihar Yobe matsalar zazzabin cizon sauro ya ragu daga kashi 42 zuwa kashi 27 cikin 100 tun daga shekarar 2013. Bayanin hakan ya fito ne daga sakataren zartarwa na hukumar kula da lafiya a matakin farko na jiha, Dokta Kundi Machina ne a wani taron manema labarai a Damaturu domin bikin ranar zazzabin cizon sauro na shekarar 2022.

Dokta Machina ya kara da cewa, an samu nasara hakan ne ta hanyar wadansu ayyuka da aka tabbatar da su a kimiyance da aka yi a jihar da suka hada da yawan rarraba gidajen sauro masu dauke da magani na rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na zamani (ITNs), da ake yi wa yara ‘yan kasa da shekaru 5 da kuma iyaye mata masu juna biyu.

“Gwamnatin jihar Yobe ta samu gagarumin ci gaba a yaki da zazzabin cizon sauro tun daga shekarar 2013 wanda hakan ya sa an samu raguwar yawan zazzabin cizon sauro. Kamar yadda hukumar NDHS ta 2013 ta nuna cewa, cutar zazzabin cizon sauro a yanzu ita ce, ke haifar da kashi 2 cikin 10 na mace-macen yara kasa da shekaru 5, sabanin kashi 30 a shekarun baya NMIS 2015 ya nuna gagarumin faduwa a cutar zazzabin cizon sauro daga kashi 42 zuwa 27 wanda abin ya ba wa ne, ci gaba a kokarin gwamnati na dakile zazzabin cizon sauro, in ji shi.

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar tare da abokan huldar sun rarraba gidajen sauro fiye miliyan 2 na dogon lokaci na Insecticidal Nets a gidan sauro (LLINs) a wani gagarumin yakin neman zabe a fadin kananan hukumomi jihar 17.

A cewarsa, shiryeshirye sun kai ga sake gudanar da wani gagarumin gangamin yakin da cutar zazzabin cizon sauro da abokan hulda wanda aka shirya za a fara a watan Agustan wannan shekara da kuma zagaye na uku na rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na zamani a kananan hukumomin 17 da ke jihar. Dokta Machina ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su kara kaimi wajen yaki da cutar zazzabin cizon sauro, yana mai jaddada cewa, dimbin albarkatun da ake bukata domin yakar annobar ba za a iya samu ba sai da jajircewar masu hannu da shuni da masu zaman kansu da kuma gwamnati. Daga kaeshe, ya gode wa abokan hadin gwiwar da suka jajirce wajen yaki da zazzabin cizon sauro.

Muhimman abubuwan da aka gabatar a cikin jawabin shi ne, gabatar da sakonnin fatan alheri daga kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) da kuma kungiyar AHNi da hadin gwiwar zazzabin cizon sauro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top