A Yobe: NDE ta horar da matasa 100 kan dabarun kasuwanci

A Yobe: NDE ta horar da matasa 100 kan dabarun kasuwanci
Tura wannan Sakon

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Hukumar kula da ayyukan yi ta kasa (NDE) reshen jihar Yobe tare da hadin gwiwar Nazeemursaj Nigeria Limited sun fara horar da matasa da mata 100 marasa aikin yi na kwanaki biyar a kan dabarun kasuwanci.

Darakta Janar na hukumar ta NDE, Abubakar Nuhu Fikpo, a lokacin da yake bayyana bude horon, ya nanata kudirin gwamnatin tarayya na ci gaba da gudanar da ayyukan ’yan kasuwa masu yawa da ke da nufin rage matakin rashin aikin yi da talauci a fadin kasar nan.

Fikpo wanda ya sami wakilcin kodineta na jihar Yobe a hukumar, John Tumba Kwaji, ya ce ana kuma sa ran shirin zai horar da mahalarta taron kan yadda za su iya rubuta rahotanni da kuma kwaikwayi yanayin kasuwa yadda ta ke. Ya ce, horon zai bai wa wadanda suka ci gajiyar damar samun lamuni daga jama’a domin inganta rayuwarsu.

A cewarsa, “Bukatar bayar da fifiko wajen bunkasa sana’o’i a karkashin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari za ta dore, domin ita ce kadai mafita ga yawaitar rashin aikin yi a Nijeriya, “Kasuwanci yana iya magance rashin aikin yi da munanan dabi’un zamantakewa da tsangwama ga matasa da karuwanci da kuma shan miyagun kwayoyi da sauransu.”

Tun da farko, daraktan sashen kananan kamfanoni (SSE) Mista Apakasa Debid wanda Misis Aisha Abubakar ta wakilta daga hedikwatar NDE ya ce, hukumar tana gudanar da sana’ar horar da matasa da mata marasa aikin yi domin su zama ’yan kasuwa masu wadata.

Ya kuma umarci mahalarta taron da su mai da hankali sosai tare da yin amfani da damar da aka ba su domin ganin sun tsaya da kafafuwansu. A madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Khadija Mohammed, ta yaba wa gwamnatin tarayya bisa wannan karimcin tare da yin alkawarin cewa, za su yi amfani da horon da aka ba su domin ganin sun zama masu tsayawa da kafafunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top