A Yobe: Rundunar ‘yansanda ta nuna damuwa kan yawaitar fade

Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
Rundunar ‘yansanda ta nuna damuwa kan yawaitar fade kan fade a fadin jihar a shekarar da ta gabata.
Bayanin hakan ya fito ta bakin ASP Dungus Abdulkarim, a ganawarsa da manema labarai a garin Damaturu, yadda ya nana ta cewa, rundunar ta yi matukar lura da hakan. A cewarsa a watan da ya gabata na Disambar 2020 an samu a kalla rahoton aikata laifin fyade kimanin 9 a bangarori daban-daban na ofisoshi.
Ya kara da cewa, a ranar 26 ga watan Disambar shekarar da ta gabata ta 2020 da misalin karfe 4.30 na Yamma rundunar su ta cafke wani mutum mai suna Malam Bako Umaru dan shekaru 35 da ke garin Geidam da laifin aikata fyade ga wata karamar yarinya ‘yar shekara 11 tare da ji mata raunuka wadda ta kai ga kwantar da ita a asibiti yayin da shi mai laifin an mika shi Damaturu sashen bincikan kwakwaf na farin kaya (CID) domin bincike a karshe kuma za a mika shi ga kuliya manta sabo domin fuskantar hukunci.
Har ila yau a ranar 25 ga watan Disamba 2020 da misalin karfe 11.00 na safe rundunar su ta cafke wadansu mutane a yankin Yindiski Musa Mohammed mai shekaru, 25 da Mohammed Dahiru dan kimanin shekaru 27 da Adamu Sa’idu mai kimanin shekaru 46 duka a garin Potiskum da laifin aikata fyade ga wata yarinya mai shekaru 13.
A wani labari mai kama da haka kuma a ranar 26 ga watan Nuwambar shekarar 2020 da misalin karfe 1:00 na rana rundunar su ta cafke Mohammed Alhaji Jajere mai kimanin shekaru 27 a Garin Gashuwa da yunkurin aikata laifin fashi wanda daga bisani suka bige da kokarin aikata fyade ga wata matar aure mai shayarwa.
A cewarsa bisa ga yadda ayyukan aikata fyade wutarsa ke kara ruruwa ya zama wajibi al’umma su hada hannu da rundunar su wajen yaki da wannan mummunan halayya ta fyade