A zabi Gawuna da Tinubu -Shugabar kungiyar

Hajiya Maryam Musa
Alhussain daga Kano
An yi kira ga al’ummar jihar Kano ranar zabe su tabbatar sun zabi mataimakin gwamnan jihar Kano, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ya zama gwamnan jihar yayin da Bola Ahmad Tinubu ya zama shugaban kasa a zaben 2023
Bayanin ya fito ne daga bakin shugabar kungiyar mata ta kasa Tinubu Gawuna Treaders Multipurpose Association, Hajiya Maryam Musa Gawuna a lokacin da take zantawa da manema labarai bayan kammala taron kungiyar kwanakin baya a Kano.
Shugabar kungiyar ta kara da cewa, matukar ‘yan takara biyu suka samu dama za su kawo wa jihar Kano da sauran jihohi ci gaba ta fannnoni da dama musamman ta fuskar kasuwancin jihar Kano da yardar Allah. Hajiya Maryam Musa
Gawuna ta ce, alamu sun nuna da yardar Allah yantakar za su nasara. Sannan kuma matsalolin da kasar nan take fuskan musamman ta fanninin tsaro zai zama tarihi saboda Tinubo da Gawuna suna da kwarewar gaske wajen tafiyar da shugabanci sun yi a baya an gani .
Ta ce, za su yi amfani da kungiyarsu wajen tallata manufofin ‘yan takarar gida gida a jihar Kano tare da wayar da kan matasa maza da mata na jihar, kuma da yardar Allah APC ita za ta kafa gwamnati tun daga kasa har sama