A Zamafara: ‘Yan-bindiga sun rantse ba za su sake sata ba

A Zamafara: ‘Yan-bindiga sun rantse ba za su sake sata ba
Tura wannan Sakon

Shu’aibu Ibrahim daga Gusau

Akalla ‘yan ta’adda bakwai ne suka tuba suka amince da shirin samar da zaman lafiya tare da rantsewa da Alkur’ani a jihar Zamfara.

Wani fitaccen dan ta’adda, Au­walun Daudawa da ya jagoranci kungiyarsa sun mika bindigo­gin AK47 20 da wadansu muggan makamai guda biyar ga gwamnan Bello Mohammed Matawalle wan­da ya mika su ga rundunar ‘yan sanda da ke jihar.

A wani takaitaccen biki da aka yi a harabar ofishin gwamnan a wannan makon, Auwalun Dauda­wa ya mika makaman tare da abo­kan aikin sa, tare da rantsuwa da Alkur’ani mai girma cewa, ba za su koma ga na su ba tsohuwar sana’ar ba ta kashe mutane da satar shanu.

Auwalun Daudawa ya ce “Ba na mika wadannan makamai ba ne don tsoron komai ba amma don imanin cewa Gwamna Matawalle mai gaskiya ne a yarjejeniyar sa ta zaman lafiya kuma ni da tawa­gata mun rungumi wannan shiri na sulhu don mun gaji da tsohu­war hanyarmu ta aikata laifi.

A fadace fadace da rikice-ri­kice da mukayi har zuwa yanzu, ban taba jin tsoron komai ba kuma ban ji rauni ba ko sau daya bisa ga wannan ina godiya ga Allah da ya sa na sami ‘yanci da rahamar sa.

Daudawa ya Kara da cewa ina neman gafara ga Allah madaukak­in sarki da Kuma al’umma Kuma ina Allah ya yarda har abada mun daina sha’awar komawa daji, muna neman Gwamna Matawalle ya bamu damar zama a Gusau.

Cikin nasa martanin, Gwamna Matawalle ya yabawa Auwalun Daudawa na rungumar zaman lafiya tare da dukkanin tawagarsa tare da yin alkawarin cewa gwam­natinsa ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba a kan alkawarin da ta yi na mutunta dukkan sharuddan da aka kulla a yarjejeniyar za­man lafiya ,kuma za ta ci gaba da jan hankalin wadanda ke daji dasu bada hadin Kai don ci gaban al’ummar jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *