A Zamfara: ‘Ƴan bindiga sun kashe mutane 4 -Sun yi garkuwa da 50

A Zamfara: ‘Yanbindiga sun kashe mutane 15 a Dutsin Gari

‘Yan bindiga

Tura wannan Sakon

Shuaibu Ibrahim daga Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe mutum hudu da garkuwa da 50 a garin Goron Namaye da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara, a cewar ‘yan sanda.

Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu da ke tabbatar da harin ga manema labarai a Gusau, ya ce, maharan sun zo babu adadi inda suka farwa garin a tsakiyar daren Lahadin da gabata.

Ya kuma kara da cewa, tuni aka tura jami’an tsaro na musamman yankin. SP Muhammad ya ce, kwamishinan ‘yan sanda CP Yakubu Elkana ya bayar da umarnin gaggauta kaddamar da binciken ganin yada za a ceto mutanen. Kuma ya umarci mazauna yankin su kwantar da hankali yayinda jami’an tsaro ke iya bakin kokarinsu wajen inganta tsaro a yankin. Ganawar Buhari da Dahiru Bauchi Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Sheik Dahiru Bauchi a fadarsa da ke Abuja.

A ranar Laraba ne babban malamain ya kai wa shugaban ziyarar sai dai babu wani rahoto da ke bayyana abin da suka tattaauna ya zuwa yanzu. Duk da cewa babu tartibin abin da suka tattauna, amma rahotanni na cewa hakan ba ya rasa alaka da kisan da aka yi wa wasu matafiya a makon da ya wuce a jihar Plateau da ke arewacin Najeriya.

Kimanin mutum talatin ne suka mutu sakamakon wani hari da ake zargin `yan kabilar Irigwe da kaiwa kan motar matafiyan a cikin birnin Jos, amma sun musanta wannan zargi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *