A Zamfara: INEC za ta dawo da rijistar masu kaDa Kuri’a a Maris

A Zamfara: INEC za ta dawo da rijistar masu kaDa Kuri’a a Maris

rijistar masu kaDa Kuri’a

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Kwamishinan zaBe na jihar Zamfara, Farfesa Sa’idu Ahmad, ya ce, hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) za ta dawo da ci gaba da rijistar masu kaDa Kuri’a a watan Maris, a fadin jihar. Ahmad ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a Gusau.

Ya ce, komawar atisayen ya biyo bayan dawo da doka da oda a mafi yawan sassan jihar da jami’an tsaro suka yi. Hedikwatar INEC ta amince da shirye-shiryenmu na ci gaba da gudanar da atisayen a dukkan ofisoshin kananan hukumomi 14 da ke faDin jihar a watan Maris.

Ya ce “Za mu juya unguwanni a Kananan hukumomin, domin bayar da dama ga masu rajista da kuma rage yawan jama’a.

“Muna farin ciki da cewa, masu ruwa da tsaki da Kungiyoyi masu zaman kansu da shugabannin gargajiya da na addini da kuma kafafen yaDa labarai, suna wayar da kan mazauna yankin da su yi rajista kafin zaBen 2023,” in ji Ahmad.

Ahmed ya ce, an gudanar da atisayen ne a shekarar 2018 da 2021 kuma ana sa ran kammala shi a ranar 30 ga watan Yuni, inda ya Kara da cewa, kashi na farko da na biyu na atisayen da aka fara a ranar 4 ga watan Janairu zai kare a watan Maris.

Ya kuma jaddada buKatar masu kaDa Kuri’a su sami katin zaBe domin samun damar kaDa Kuri’a a zaBe mai zuwa. “Yana da kyau a san cewa, INEC ta Bullo da sababbin abubuwa a cikin atisayen, waDanda suke buKatar Daukar hotunan yatsu da fuskokin duk masu rajista.

“Haka kuma, yanzu za a iya fara rajistar ta yanar gizo tare da kamawa da za a yi a dukkan ofisoshin INEC 14,” in ji REC. Ahmad ya ce, hukumar ta Kara yawan rumfunan zaBe daga 2,516 zuwa 3,529.

Wannan ya yi daidai da manufar shugaba Muhammadu Buhari da kuma dalilin da ya sa ya sanya hannu kan dokar zaBe ta 2022 da aka daDe ana jira ta zama doka. “Bayan sanya hannu kan dokar zaBe da aka yi wa kwaskwarima, hukumar ta fitar da jadawalin da jadawalin ayyukan babban zaBen 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *