A Zamfara: Iyaye sun ce ‘ya’yansu sun fara manta karatu

Iyaye sun ce ‘ya’yansu sun fara manta karatu
Iyayen yara a jihar Zamfara, sun yi kira ga gwamnati da ta dubi yi wuwar bude makarantu domin hana dalibai ci gaba da gararamba kan titi.
Makarantun firamare da na sakandare a jihar sun kasance a rufe kusan wata biyu, a wani bangare na tsaurara matakan yaki da ‘yan bindiga da suka bullo da salon satar dalibai a makarantu.
Tun a ranar 1 ga watan Satumbar 2021, ne gwamna Bello Muhammad Matawalle, ya sanar da rufe makarantu, kama daga firamare har sakandare, ya Allah jeka ka dawo ko na kwana da ke fadin jihar.
Hakan ya biyo bayan zafafa kai hare hare a makarantun sakandare har ma da na gaba da su.
Matakin gwamnatin na daukar wannan mataki ya zo ne jim kadan bayan sace daruruwan daliban makarantar sakandare da ke Kaya a karamar hukumar Maradun.
Kuma harin ya zo ne kasa da mako guda bayan sako daliban kwalejin kimiyyar noma da kiwo da ke Bakura.
Tuni dai wasu iyayen yara suka fara nuna fargaba kan yadda ba bu wani bayani da ke fitowa daga bakin hukumomin jihar kan batun bude makarantu, duk da samun haske a yaki da ‘yan bindigar.
Wani mahaifin daya daga cikin daliban da ke karatu a jihar ta Zamfara ya shaida wa BBC cewa, ‘yarsu har ta fara manya karatu, kuma ganin haka a yanzu shi da mahaifiyar yarinyar ne ke koyawa ‘yar ta su karatu a gida.
Mutumin ya ce, yakamata gwamnati ta dubi wannan yanayi da dalibai a jihar ke ciki, domin in banda gararanba ba bu abin da wasu daliban ke yi.
Ita ma wata mata da BBC ta ji bakinta a kan rashin bude makarantu a jihar ta Zamfara, ta ce yakamata gwamnatin jihar ta su ta kalli abin da gwamnatin jihar Kaduna ta yi wajen bude makarantu duk da satar daliban da ake yi a jihar.
Matar ta ce,” Gwamnatinmu ta dauki mataki irin Kaduna, a samar da tsaro a makarantu sannan sai a bude su don yara su ci gaba da karatu”.