A Zamfara: Kungiyar ’yan fansho ta koka

Gwamna Bello Matawalle
Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Kungiyar ’yan fansho ta Nijeriya, reshen Zamfara, ta roqi gwamna Bello Matawalle da ya gaggauta sake duba kudaden fansho zuwa mafi qaranci Naira dubu 30. Shugaban qungiyar, Hassan Muhammad Gusau ya yi roqon a cikin saqon murnar zagayowar ranar ‘yan fansho ta shekarar 2021 a Gusau.
Ya qara da cewa, wadansu daga cikin qalubalen da qungiyar ke fuskanta sun hada da qin mutunta ‘yan fansho da gangan musamman ma qa’idojin da tsarin mulki ya tanada a cikin sashe na 173 da na 210 na kundin tsarin mulkin na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
Ya ci gaba da cewa, a rinqa yin bitar dokar fansho duk bayan shekara biyar tare da qarin albashin ma’aikata ko kuma wanda ya zo na farko.
Ya ce, gwamna Bello Matawalle ya yi alqawarin ci gaba da fitar da tallafin Naira miliyan 100 ga ‘yan fansho na jiha da na qananan hukumomi kowanne wanda har yanzu ba a fara aiwatar da shi ba. Shugaban ya ce, wani qalubalen shi ne, ‘yan fansho da ke da kaso na tarayya na fansho da PTAD ke tantancewa, yanzu ta hanyar fasahar sadarwa ne ko kuma ta yanar gizo,” in ji shi.
Ya yi bayanin cewa, ana ci gaba da biyan fansho na bayar da gudunmawa ga wadanda suka cancanta. Ya ce, rashin samun mafi qarancin fensho yana da matuqar takaici domin har yanzu ’yan Daga shafi na farko Wannan yarinyya bata ta yi, a taimaka mana da cigiya. Sunanta Fatsima. A Naibawa ‘Yan Lemo gidansu yake. Ga lambar mahifinta Abubakar Mustapha 08067213986. fansho da yawa suna karbar qasa da Naira dubu 3 a wata.
Domin haka qungiyar qwadago ta yi kira da a sake duba kudaden wanda ba a yi ba tun shekarar 1999, inda ya ci gaba da cewa, sauya garatuti na ’yan fansho gaba daya da kuma qara mafi qarancin albashi a jihar zuwa aqalla Naira dubu 30 a wata, qungiyar ta tabbatar wa ‘yan qungiyar cewa, za ta ci gaba da qoqarin kyautata jin dadin ‘ya’yanta.