A Zamfara: Majalisar Dokoki ta gayyaci masu ruwa-da-tsaki -Kan aikin filin jirgi

Matawalle ya zama jagoran APC a Zamfara

Bello Matawalle jagoran APC a Zamfara

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Alhaji Nasiru Mu’azu Magarya a yau ya jagoranci wadansu shugabannin kwamitocin majalisar, zuwa tashar jirgin saman kasa da kasa ta Gusau domin gudanar da aikin sa’ido.

Kakakin ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda aikin yake tafiya ya kuma yi kira ga ma’aikatar kula da gidaje da raya birane da takwararta ta ayyuka da na sufuri da mai bayar da shawara kan aikin, BJ Auronotricts da sauransu.

Kiran ya fito ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Darekta Janar na hulda da jama’a na majalisar dokokin, Mustafa jafaru Kaura, wanda aka raba ta ga manema labarai a Gusau.

Ya kuma bayar da umarnin a gayyaci dukkan masu ruwa da tsaki na aikin filin jirgin zuwa ofishinsa a mako mai zuwa domin bayyana abin da ya kawo jinkirin aikin da matsalolin kudi da kuma hanyoyin da majalisar za ta sa baki, domin ganin cewa, aikin bai samu matsala ba. In ji shi. . Kakakin majalisar Magarya ya jinjina wa kokarin da gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun ya ke yi na ganin ya tabbatar da mafarkin mutanen Zamfara na samar da filin jirgin sama na kasa da kasa.

A yayin da yake gudanar da ziyarar, Kakakin majalisar da tawagarsa da suka gudanar da ziyarar sun hada da kwamishinan gidaje da raya birane na jihar, Alhaji Ahmad Muhammad Muktar Gusau, ya kuma shaida wa kakakin majalisar jihar cewa, ma’aikatarsa ba za ta bar wani abu ba wajen ganin an kiyaye daftarin kudirin. Ya kara da cewa, ma’aikatarsa na gudanar da ziyarar aikin mako-mako tare da mai bayar da shawara kan aikin, domin tabbatar da bin ka’ida.

Alhaji Ahmad wanda ya bayyana kwarin gwiwar cewa, za a kammala aikin a kan kari, ya ce, ruwan sama mai karfi a lokacin damina ne ya janyo tsaikon gudanar da aikin, ya kuma jaddada cewa, bayan kammala kakar aikin an fara aiki da gaske kamar yadda kakakin majalisar ya shaida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *