A Zamfara: Marafa ya yi tir da kai wa ‘ya’yan PDP hari

A Zamfara: Marafa ya yi tir da kai wa ‘ya’yan PDP hari

Senator Marafa

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Tsohon Sanata, Kabiru Garba Marafa na jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya yi Allah-wadai da kakkausar murya dangane da harin da aka kai kan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP a yayin taron gudanar da zaben shugabannin ta na jiha.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Sanata Marafa a jam’iyyar APC, Bello Bakyasuwa Maradun, ya rarraba ta ga manema labarai.

Bello Bakyaauwa, ya ce Sanata Marafa na jam’iyyar APC a karkashin jagorancin shugabanta, Sirajo Garba Maikatako, sun kadu da suka samu labarin tashin hankalin da aka yi wa jam’iyyar adawa ta PDP a yayin taron jam’iyyar a Gusau.

Bakyasuwa ya ce, “Mun fi damuwa da yadda wadansu kalamai a hukumance da aka danganta ga mai magana da yawun mataimakin gwamnan jihar Zamfara wanda daya ne daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar na alakanta matakin da jam’iyyar APC mai mulki a jihar”.

Ya ce “Duk da cewa, sanarwar ta yi nuni da yatsa ga ‘yan barandar bangaren gwamna Bello Matawalle na jam’iyyar APC suka shirya, muna amfani da kafar wajen kawar da bangaren Sanata Marafa na APC daga aika-aikan rashin bin tafarkin dimukradiyya ga ‘yan adawa”.

Bakyasuwa ya jaddada cewa, a rubuce yake cewa, Sanata Kabiru Marafa (CON) mai kare dokoki da bin doka da ka’ida A Zamfara: Marafa ya yi tir da kai wa ‘ya’yan PDP hari ne, daga shaidar ayyukan da ya yi a bainar jama’a a matsayinsa na Sanata na Jamhuriyar Nijeriya da jigo a jam’iyyar APC a jihar Zamfara. Ya kara da cewa, “A kan haka, shugabancin bangaren Sanata Marafa na APC, ya yi Allah wadai da matakin da aka dauka a kan jam’iyyar adawa ta PDP a jihar baki daya, tare da daukar matakin na dabbanci da babu tsautsayi “in ji shi.

“Muna kira ga shugabannin ‘yan sanda a matakin jihohi da na shiyya da na kasa da su binciki lamarin sosai tare da sanya masu laifin da masu daukar nauyinsu su fuskanci fushin doka da ya dace”.

Hakazalika muna kira ga ‘yan sanda da su yi amfani da lamarin a matsayin jajayen tuta kuma su kasance cikin shiri domin gujewa faruwar irin mummunan aiki na ‘yan siyasa masu son zuciya ba tare da tsoro ko fargaba ba”.

“A matsayinmu na ‘yan dimukradiyya, muna yaba halin da jam’iyyar adawa ta PDP ta yi da aka nuna wajen fuskantar tashin hankali da tafiyar da al’amura”. “Muna taya su murna da gudanar da taro tare da fitowa da sababbin shugabannin jam’iyyar jihar”.

“Duk da haka, muna fata cewa, a kan lokaci sabon shugabancin jam’iyyar PDP a jihar za su fahimci manufofin ci gaba na jam’iyyar APC musamman irin jajircewar Sanata Marafa na gina jam’iyyar domin ceto jihar Zamfara daga kangin rashin tsaro”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *