A Zamfara: PDP ta bukaci Matawalle da ya yi murabus

Alaka da ‘yan-fashi: Gwamnan Zamfara ya dakatar da sarkin Dansadau

Gwamnan Zamfara Bello Matawale

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara, Farfesa Kabir Jabaka, ya yi kira ga gwamna Bello Matawalle da ya yi murabus, domin ceto jihar daga ci gaba da yin garkuwa da mutane da kashe-kashen da ake yi a jihar.

Jabaka ya yi kiran ne a lokacin da yake jawabi ga manema labarai kan matsalar tsaro a jihar a sakatariyar jam’iyyar PDP ta jihar da ke Gusau a ranar Litinin.

Ya ce, “Akwai isassun shaidu da ke nuna cewa, shugabancin da ke kan mulki a jihar bai damu da yadda ake tabka asarar rayuka ba, da ci gaba da kone-konen kayayaki da abinci a kusan kowace al’umma a fadin jihar.

Ya bayar da misali da ziyarar da gwamnan ya yi a jamhuriyar Nijar a kwanakin baya domin halartar bikin kokawa inda ya nuna kansa a matsayin dan kallo mai mutunci.

Ya ce, Matawalle ya shagaltu da kallon bikin kokawa na shekara-shekara a jamhuriyar Nijar, ya bar al’ummar jiharsa cikin fargabar ‘yan fashi da makami da yunwa da talauci,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *