A Zamfara: Shin nada, Aleru sarauta zai kawo zaman lafiya?

A Zamfara: Shin nada, Aleru sarauta zai kawo zaman lafiya?

Aleru

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

A ranar Asabar da ta gabata gwamnatin jihar Zamfara, karkashin jagorancin Bello Matawalle ta nada daya daga cikin kasurgumin dan fashin daji da aka fi sani da suna Ado Aleru a matsayin sarkin Fulanin ‘Yandoto.

Ado Aleru sarkin Fulani gwamnatin jihar Zamfara ce ta ba shi sarautar, wanda wadansu suke ganin ta yi hakan ne domin ta jawoshi a jiki ko Allah zai sanya a sami zaman lafiya.

Idan ba’a manta ba, Ado Aleru shi ne wanda gwamnatin jihar Katsina ta sanya cewa, duk wanda ya kawo shi za ta ba shi miliyan 5, sakamakon yadda ya addabi al’ummar jihar Katsina.

Abin da jama’a ke tambaya a nan shi ne, sabon sarkin Fulani Aleru zai cika alkawari jama’ar Tsafe da Munhaye da sauran yankuna zai barsu su zauna lafiya a matsayinsa na sarkin Fulani a yanzu.

Kafin karamci da gwamnati ta yi wa Ado Aleru sai da ta fitar da makuden kudade domin shirya wasan Sallah tsakanin manyan ‘yan fashin daji Fulani da yaransu da kuma manoma suka zo filin wasa a Gusau, an yi an tashi lafiya.

Abin tambaya a nan shi ne, ko su ‘yan bindigar za su cika alkawari su bar mutane su zauna lafiya, duk da abin da gwamnati take yi masu na karamci, idan ba’a manta ba, gwamna Bello Matawalle  da ya ga fitinar ta yi yawa  ya ce, kowa ya kare kansa ya kuma bayar da dama mutane su mallaki bindigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *