A Zamfara: Takala tsakanin ‘yan Matawalle, ‘yan Marafa ta kunno kai

A Zamfara: Takala tsakanin ‘yan Matawalle, ‘yan Marafa ta kunno kai

Matawalle da Marafa

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Ganin yadda guguwar siyasar ke tashi a jihar Zamfara, bangaren siyasar gidan siyasar Kabiru Marafa na zargin bangaren gwamna Matawalle da daukar sabon salo musamman amfani da ‘yan bangar siyasa wajen afkawa abokan adawarsu a duk mako.

Sakataren yada labaran APC, bangaren Sanata kabiru Garba Marafa, Honarabul Bello Bakyasuwa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin jam’iyar da ke Gusau babban birnin jihar.

Bakyasuwa ya ce, wasu ‘yan daba sun kai wa shugaban dandalin sada zumunta na Sanata kabiru Garba Marafa, Shamsu Shehu wanda aka fi sani da (Shamsu Kasida) hari, wanda bisa ga dukkan alamu ‘yan bangaran siyasa ne na gwamnan jihar Bello Matawalle.

Ya ce, wannan al’amarin ya auku ne a ranar Juma’a 14 ga watan Janairu, 2022 inda aka kai wa Kasida hari a wani wuri daura da gidan gwamnatin jiharda ke Gusau. Ya kara da cewa bayan kai harin, Kasida ya sami munanan raunuka kuma sun lalata motarsa, inda daga bisani suka shige gidan gwamnati nan take don samun mafaka cikin kwanciyar hankali.

Bello ya ce, “A madadin jam’iyyar APC karkashin jagorancin Surajo Garba Maikatako Gusau, muna Allah wadai da irin wannan ta’addanci da rashin wayewa da bangaren jam’iyyar APC karkashin jagorancin Matawalle da gwamnatinsa suke dauka ta hayar ‘yan bangar siyasa domin su afkawa abokan adawarsu da masu sukansu domin kawai su rufe bakin duk wanda yake da damar tona asirinsu”.

Ya ci gaba da cewa, “‘Yan bangar siyasar da suka kai hari kan Kasida sun sami kayan aikin ne daga bangaren Matawalle na jam’iyyar APC da gwamnatinsa, don su yi amfani da shi wajen yakar bangaren Marafa, idan ba haka ba ta yaya ‘yan dabar za su kai wa shugabanmu na (social media) hari daura da gidan gwamnatin jiha, kuma su shiga cikin gidan kai tsaye ba tare da wata turjiya daga jami’an tsaro ba”? Bakyasuwa ya ce, “Idan kuna iya tunawa wannan ba shi ne karon farko da wasu ’yan daba na Matawalle suke kai hari kan mabiya Marafa ba, a lokacin taron zaben kananan hukumominmu a watan Disambar bara, ’yan bangar Matawalle sun far wa mutanenmu wadanda kawai suke aiwatar da aikin da tsarin mulki ya ba su.

A kan haka muke jawo hankalin kwamishinan ’yan-sandan jihar nan da gaggawa da su kamo tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin, idan ba haka ba za a tilasta mana daukar matakin da ya dace kamar yadda dokar kasa ta tanada”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *