A Zamfara: ‘Yan-bindiga sun sace Kanar ‘Yandoto

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Wadansu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da Kanar Rabi’u Garba ‘Yandoto (mai ritaya) da ‘ya’yan cikinsa guda biyu a hanyar Gusau zuwa Tsafe a jihar Zamfara.
Kanar Rabi’u an daukeshi bayan ya gama jawabi a gidan Radiyon FM na Farin wata da ke Gusau, kan hanyarsa ta koma wa gida a Tsafe.
Wani dan yankin mai suna Mohammed Hassan” ya bayyana cewa, ‘Yandoto na tafiya garinsu tare da ‘ya’yansa biyu a daren ranar Lahadi, inda ‘yan bindiga suka yi masa kwanton bauna suka kama shi suka shiga daji da shi “.
“Mun ji karar harbe-harbe kuma muka fara gudu zuwa cikin daji saboda tsoron ‘yan bindigar amma daga baya muka gane cewa, shi kawai suke so su dauka” in ji shi Sai dai daukar ‘Yandoto ya kawo cecekuce a fadin jihar tare da danganta sace shi da maganganun da ya yi kan Sanata Kabiru Garba Marafa wanda babu jituwa tsakaninsu na tsawon shekaru.
Wata majiya ta shaidawa wakilinmu cewa, Rabi’u Garba shi ne shugaban kungiyar siyasar Zamfara ta APC mai suna “Wake da Shinkafa” da nufin ganin Kabiru Marafa bai lashe kujerar Sanata ba a zaben shekara 2023 ba. Yin wake da shinkafa na nufin zaben Bello Muhammad Matawalle na APC a matsaayin gwamna sai su zabi Ikra Aliyu Bilbis na PDP a matsayin Sanata mai wakiltar Gusau da Tsafe.
Har zuwa lokacin rubuta labarin babu wata magana da gwamnati ko daga su wadanda suka dauke shi.