A Zamfara: ‘Yanbindiga sun kashe mutane 15 a Dutsin Gari

‘Yan bindiga
Shu’aibu Ibrahim daga Gusau
Duk da irin tashin hankalin da al’ummar kauyen Dutsin Gari ke ciki na dauke wadansu masallatan Juma’a a kwanakin baya, sai ga wani sabon hari da suka sake tsintar kansu a ciki a wannan makon wanda har ya yi sanadiyar kashe mutane 15.
‘Yan bindigar sun sake shigowa garin Dutsin Gari da Rayau da ke karamar hukumar Maru, kamar yadda wani shaidun gani da idanu ya bayyana wa manema labarai ta wayar tafi da gidan ka, Malam Ibro Mamman wanda ya ce ‘yan fashin da ke kan babura sun mamaye kauyen Dutsin Gari a daren jiya da niyyar yin garkuwa da wadansu mutane amma mazauna garin sun yi alwashin ba za su sake bari a dauki wani a garin ba suka fuskance su har suka fatattake su, mutanen kauyen sun gwabza da ‘yan fashin inda suka dauki tsawon awanni ana artabu.
Mamman ya ce lokacin da ‘yan fashin suka fahimci haka, ba za su iya yin nasara a cikin mummunan aikinsu ba, sai suka bude wuta inda suka kashe mutane 15, suka ji wa da dama rauni sannan suka koma wani kauye da ke kusa da ake kira Rayau “.
“A kauyen Rayau, ‘yan bindigar sun kuma fuskanci irin wannan kalubalen daga mazauna kauyukan wadanda suke a shirye domin karbar labarinka abin da ya faru a kauyen Dutsin Gari’
“Mazauna kauyen sun fito da yawa sun yi artabu da ‘yan bindigar inda biyu daga cikin mutanen garin suka rasa rayukansu kuma ‘yan bindigar suka tafi ba tare da sun kame kowa ba”. In ji Mamman.
Malam Mamman ya ce, ‘yan fashin sun sake komawa kauyukan da sanyin safiyar yau domin sun gano cewa, mazauna kauyukan da yawa sun bar garin sun gudu zuwa garin Kanoma saboda tsoron abin da zai je ya dawo, a dawowar na su sun bankawa gidaje da yawa wuta sannan suka tafi da dabbobin jama’a.
Idan za ku iya tuna wa cewa, a wadansu watanni a baya ‘yan bindigar sun shiga garin inda suka yi awon gaba da masallata masu sallar Juma’a su 40 ciki har da Limamin kauyen Dutsin Gari lokacin da ake sallar Juma’a a wani lokaci a baya.
An yi kokarin yin magana da kakakin rundunar ‘yan sanda, SP Mohammed Shehu, amma bai dauki kiran wayar ba.