A Zamfara: Za a ci gaba shari’ar Marafa

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Wata babbar kotu da ke jihar Zamfara karkashin jagorancin mai shari’a, Bello Kucheri ta dage sauraron kararraki uku da Sanata Kabiru Garba Marafa ya shigar kan jam’iyar APC, inda suke kalubalantar halaccin mai Mala Buni da ya kaddamar da kwamitin riko.

Hakan ya biyo bayan kin bayyanar lauyoyin Sanata Marafa na zuwa kotun kamar yadda bangarorin biyu suka amince a ranar 17 ga watan Fabrairun 2022.

Da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan dage ci gaba da shari’ar, lauyan Sanata Kabiru Garba Marafa da Barista Musbau Salawudden, ya ce, babban lauyan, Barista John Shaka ya rubuta wa alkalin alkalan jihar, mai shari’a Kulu Aliyu kan suna bukatar isasshen tsaro kafin a ci gaba da aikin.

A cewarsa, kowa ya san abin da ya faru a zaman karshe da aka yi a kotun a ranar 17 ga watan Fabrairun 2022 lokacin da wadansu ‘yan bangar siyasa suka mamaye kotun suka kai hari kan daya daga cikin lauyoyin da kuma sakataren yada labaran Sanata Kabiru Marafa da Bello Bakyasuwa.

Ya ci gaba da cewa, “An gudanar da shari’ar da kotu ta yi a dukkan wadannan shari’o’in cikin lumana ba tare da wata tangarda ba, an kuma dage shari’ar zuwa ranar 14/3/2022 domin ci gaba da nazari a ranar.

Ya ce, bayan fitowa kotu “Ana cikin hira da manema labarai sai ‘yan bangar siyasa suka yi ta kururuwa suna amfani da kalamai na batanci da nufin tayar da kayar baya, bayan sun kutsa kai cikin harabar kotun.

Daga nan suka fara dukan motar daya daga cikin lauyoyin Sanatan , domin gudun kada rikicin ya barke, sai lauyan ya yi gaggawar ficewa daga harabar kotun zuwa wani wuri mai nisa.

Daga karshe, lauyoyin Sanatan sun aika da wasiku zuwa ga alkalin alkalan jihar kimanin kwanaki uku bayan zaman kotun a ranar 17 ga watan Fabrairun 2022 kuma har ya zuwa yanzu babu amsa daga babban alkalin alkalan jihar, Hajiya Kulu Aliyu wanda ke nuna rashin bin dokar jihar gaba daya.” In ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top