A Zariya: Sarkin dillalan Tudun Wadan zai yi takarar majalisar Kaduna

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

A wannan makon ne Alhaji Shehu Ahmed, Sarkin Dillalan Tudun wadan Zariya ya kasance a ofinshin jam’iyyar NNPP, inda bias jagorancin shugaban jam’iyyar na jihar Kaduna Mista Ben Kure ya sayi takardar tsaya takarar majalisar jihar Kaduna a maabar Zariya – kewaye, a zaben shekara ta 2023.

Bayan ya mika wa Sarkin Dillalan Tudun Wadan Zariya takardar takarar da ya saya, shugaban jam’iyyar Mista Ben Kure, ya fara da nuna jin dadinsa na yadda fitaccen matashi kuma dan siyasa ya bayyana kudurinsa na yin takar a zabar da aka ambata.

Mista Ben ya kara da cewar, samun fitaccen mutum kamar Alhaji Ahmed Shehu a jam’iyyar NNPP, babbar nasara ce da ta fara bayyana a wannan jam’iyyar, kafin ma zaben shekara ta 2023 da jam’iyyar NNPP za ta gwada kashi da sauran jam’iyyu da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi ma su rijista.

Da kuma ya juya ga Alhaji Shehu Ahmed, Sarkin Dillalan Tudun Wadan Zariya, sai ya shaarce da cewar, ya ci gaba da neman al’umma su ba shi damar wakiltarsu a majalisar jihar Kaduna, kamar yadda ya dora – dambar yi daga lokacin da ya sayi takardar takara, kamar yadda tsarin jam’iyyar ta tanada a kudinta.

A zantawar da wakilinmu ya yi da Alhaji Ahmed Shehu bayan ya sayi takardar takara, ya fara da karyata zantukan da ake yada wa cewar, ba zai yi takara ba a mazabar Zariya – Kewaye ba, a nan sai ya ce, sayen takardar da ya yi, dukkanin kalaman da ake yadawa cewar ba zai takara ba, ta zama tarihi.

A cewar Sarkin Diilan Tudun Wadan Zariya, batun takara sun runguma da hannu biyu, duk wasu kalamai na suke fitowa daga ‘yan adawa, ba zai sa gwiwoyinsu su yi sanyi ba, wadannan kalamai, a cewar, tamkar kaimi da ake yi doki, na kara mikewa domin tunkarar zaben shekara ta 2023, in mai duka ya kai mu.

Da kuma ya juya ga al’ummomin da suke gundumomi bakwai da suke mazabar Zariya – Kewaye, sai tabbatar ma su da cewar, in har suka bas hi daman wakiltarsu a majalisar jihar Kaduna, babu ko shakka, a cewarsa, za su ga wakilcin da ba su taba gani ba, na samar da wakilcin da al’umma ne a gaba na bayyana abubuwanda suke bukata gwamnatin jihar Kaduna ta yi ma su.

ya ce a matsayinsa na wakilinsu, ofishin tuntuba da zai bude bayan samun nasara, zai zama mahada a tsakaninsa da al’ummar da ya ke wakilta, in ba sh a kusa, daraktocinsa za su wakilce shi a duk lokacin da al’umma suka nemi yin tozali da shi. Kwamared Mas’ud Kabir wanda ke zama babban daraktan Sarkin Dillalai Alhaji Shehu Ahmed, cewar ya yi, tun farko sun sayi fom na takarar ne, saboda kiraye – kirayen da al’ummar wannan gunduma ta waje mai gundumomin kansila guda bakwai suka yi wa Alhaji Ahmed Shehu, ya yi takara da zai wakilce su a majalisar jihar Kaduna a zabe mai zuwa.

A karshe Kwamared Mas’ud yay i kira ga al’umma gundumar waje da su ci gaba da ba su shawarwarin da kuma yin addu’o’in da za su zama silar samun nasara a zabe mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *