A Zariya: Shugabannin NUT sun yi tazarce

A Zariya: Shugabannin NUT sun yi tazarce

A Zariya: Shugabannin NUT sun yi tazarce

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

A ranar talatar da ta gabata ce, daukacin shugabannin kungiyar malaman makaranta ta Nijeriya [ NUT ] reshen karamar hukumar Zariya, suka sami nasarar ci gaba da shugabancin kungiyar nan da shekara hudu ma su zuwa.

 Tabbatar da amince wa shugabannin su ci gaba da jagorantar kungiyar ya gudana ne a kwalejin Alhuda – Huda da ke birnin Zariya bisa jagorancin shugabannin kungiyar na kasa reshen jihar Kaduna, A jawabinsa jim kadan bayan an tabbatar ma sa da ci gaba da jagorancin kungiyar, Kwamared Yahaya Abbas, da farko ya nuna matukar jin dadinsa na yadda daukacin wakilan kungiyar sun tabbatar da cewar ya cancanci ci gaba da shugabancin kungiyar, sai ya kara da cewar, wannan dama da aka sake ba shi, tamkar kaimi aka yi ma sa tare da ayrinsa, na su kara tashi tsaye, domin aiwatar da ayyukan da za su ciyar da malamai da ilimi da kuma duk wani bangare na ilimi gaba.

 Da kuma ya ke tsokaci kan nasarorin da suka samu duk da karancin ma su gidan rana da suka fuskanta, Kwamared Abbas ya ce sun sami nasarori na ayyukan da suka yi fiye da guda 43, da suka hada da biyan alawus ga ma su kula da tsaron ofishin malaman da biyan alawus ga ma’aikatan da suke aiki a reshen kungiyar da ke Zariya.

Sauran nasarorin da Kwamared Yahaya Abbas ya ce sun samu sun hada da samun damar halartar taron kungiyar da kundin tsarin kungiyar ya tanada da yadda suka yi ammafani da ma su gidan rana wajen tarzomar lumana kan korar malamai da gwamnatin jihar Kaduna ta yi da nasarar da suka samu na hada sunayen daukacin malaman da matsalar korar malaman ta shafa inda aka mika sunayensu da sauran bayanansu ga hukumomin da suka dace, domin warware matsalolin da malaman suka tsinci kansu a ciki.

Game da inganta ofishin kungiyar kuma Kwamared Yahaya Abbas ya kara da cewkar sun sayi sabbin kujeru da amsa ku – wa da bayar da tallafin kudi ga wasu malamai da rashin lafiya ya same su da bayar da tallafin kudi ga wasu malamai da suka sami matsalar rashin samun albashin da suka saba samu. A dai jawabinsa ya tabbatar da cewa, shugabannin kungiyar za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa, na ganin sun yi amfani da tsarin mulkin kungiyar ya tanada na ganin an kare mutuncin duk wani malami ako wani hali da dokar aikin gwamnati ya tanada.

 Da kuma Kwamared Yahaya Abbas ya juya ga daukacin malamai na karamar hukumar Zariya, ya yi kira garesu da su ci gaba da yin aiki tukuru fiye da yadda suke yi a halin yanzu, domin ci gaban ilimi a karamar hukumar Zariya baki daya. A cewarsa shugabannin kungiyar ako wane lokaci su na shirye ako wane lokaci, na ganin sun rungumi duk wata matsala da ke addabar malaman domin su sami damar sauke nauyin da aka dora ma sun a kula da koyar da yara da kuma tarbiyyarsu kamar yadda suke yi a halin yanzu.

A dai lokacin wannan taro na amincewa shugabannin kungiyar malaman su ci gaba da jagorantar kungiyar an amince Kwamared Yahaya Abbas ya ci gaba da zama shugaban kungiyar sai Shehu Abdulkadir Aliyu Na’ibin shugaba sai Mahmud Aliyu Isa a matsayin mataimakin shugaban kungiyar na farko sai mataimakin shugaban kungiyar na biyu aka tabbatar da Sagir Abubakar Kusfa sai Jamila Muhammad Lawal mataimaki yar shugaba ta uku sai sakataren kungiyar aka tabbatar da KasimuMuhammadLawal sai Muhammad Abdulkadir Shitu ya ci gaba da zama a kujerar mataimakin sakatare sai Aminu Shehu , kujerar ma’aji sai Hauwa’u Musa Lukman skatariyar kudi sai jami’in watsa labarai aka tabbatar da Muhammad Tasi’u Adamu sai jami’in watsa labarai aka gtabbatar da Alhassan Sama’ila Nabara sai Asma’u Umar sai mai binciken lalitar kungiyar na farko da na biyu aka zabi Asma’u Umar da kuma Mannir Ibrahim.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *